Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Isra'ila ta tura tawaga don tattaunawar tsagaita wuta ta biyu a Qatar

Yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da yankin Gaza ta shiga kwana na 17 — bayan dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 47,500. Kazalika Netanyahu ya tafi Amurka domin tattaunawa da Trump. 1132 GMT — Isra'ila ta ce za ta tura wata tawaga ta sasantawar zagaye n...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta tura tawaga don tattaunawar tsagaita wuta ta biyu a Qatar
At a glance

Yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da yankin Gaza ta shiga kwana na 17 — bayan dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 47,500. Kazalika Netanyahu ya tafi Amurka domin tattaunawa da Trump. 1132 GMT — Isra'ila ta ce za ta tura wata tawaga ta sasantawar zagaye n...

Yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da yankin Gaza ta shiga kwana na 17 — bayan dakarun Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 47,500. Kazalika Netanyahu ya tafi Amurka domin tattaunawa da Trump. 1132 GMT — Isra'ila ta ce za ta tura wata tawaga ta sasantawar zagaye na gaba a batun tsagaita wuta tsakaninta da Hamas, tana mai ba da alamar samun cigaba gabanin ganawar Firaminista Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka Donald Trump. Netanyahu zai zama shugaban wata ƙasar waje na farko da zai gana da Trumo a Fadar White House tun bayan komawarsa mulki a watan da ya gabata, kuma akwai yiwuwar zai fuskanci matsin lamba kan amincewa da tsagaita wutar da shugaban Amurkan ke ikirarin shi ya tsara. Awanni kafin ganawar tasu, ofishin Netanyahu ya ce Isra'ila za ta tura wata tawaga zuwa Doha babban birnin Qaatar nan gaba a cikin makon nan don tattaunawar. Hamas ta ce a shirye take ta sasanta a mataki na biyu na tsagaita wutar da Qatar da Masar da Amurka ke shiryawa, wadda kuma za ta mayar da hankalu a kan samar da mafita ta dindindin ga yaƙin. 1154 GMT — Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi gargadi kan sake fara kai hare-hare a Gaza da Netanyahu zai yi Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bukaci kasashen duniya da su dauki matsaya guda tare da hana Netanyahu sake fara wani kisan kiyashin domin cim ma wata manufa ta siyasa. Ya kuma bayyana cewa akwai tambayoyi a duniya game da yadda gwamnatin Netanyahu za ta kasance bayan sakin fursunonin Isra'ila. 1150 GMT — Gwamnatin Falasdinu ta kafa kwamitin da zai tafiyar da yankin Gaza bayan yakin Gwamnatin Falasdinu ta kafa "kwamitin aiki" don kula da Gaza bayan yakin kisan kare dangi na Isra'ila. "Gwamnatin Falasdinu karkashin jagorancin Shugaba Mahmoud Abbas ta yanke shawarar kafa wani kwamiti mai aiki da zai kula da al'amuran Gaza," in ji Firaminista Mohammad Mustafa a wani taron majalisar zartarwa. “Gwamnati…tana kokarin gaggauta kai kayan agaji da bude hanyoyi da kawar da baraguzan gine-gine, da samar da wuraren taruwar da suka dace domin tsugunar da wadanda aka lalatar da gidajensu, a shirye-shiryen sake gina yankin.”