Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Isra'ila ta tsare Falasɗinawan Gaza waɗanda ke fama da tsananin rashin lafiya

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 451 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,514 tare da jikkata fiye da mutum 108,189. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,048 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 2259 GMT — Sojojin Isra'ila sun tsare wasu Fala...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta tsare Falasɗinawan Gaza waɗanda ke fama da tsananin rashin lafiya
Kwa muhtasari

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 451 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,514 tare da jikkata fiye da mutum 108,189. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,048 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 2259 GMT — Sojojin Isra'ila sun tsare wasu Fala...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 451 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 45,514 tare da jikkata fiye da mutum 108,189. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,048 tun da ta soma kai hare-hare a Oktoban 2023 2259 GMT — Sojojin Isra'ila sun tsare wasu Falasɗinawa marasa lafiya huɗu a lokacin da ake kan hanyar kau su Birnin Gaza daga arewacin Gaza domin yi musu magani, in ji ma'aikatar lafiya ta yankin. Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ce "dakarun mamaya sun tsare marasa lafiya hudu cikin 10 a yayin da Hukumar Lafiya ta Duniya ke tafe da su a hanya don karbar magani daga Asibitin Indonesiya da ke arewacin Gaza zuwa Asibitin Al-Shifa da ke birnin Gaza." Ma'aikatar ta kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin ma'aikatan na cikin mawuyacin hali. 2334 GMT — Ministar Sadarwa na Isra'ila ya afka Masallacin Al-Aqsa Ministan Sadarwa na Isra'ila Shlomo Karhi tare da rakiyar Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna da suka mamaye yankunan Falasdinawa, sun afka masallacin Al-Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye. Karhi ya gudanar da ibada a daya daga cikin ramukan da ke karkashin bangon Yamma (bangon Al-Buraq) sannan ya yi tsokaci kan kutsen da aka yi wa X. "A cikin wadannan kwanaki da sojojin Isra'ila ke samun nasara ta kowace fuska, na tuna da abin da Midrash (nassosin addini na Yahudawa) suka ce: 'A nan gaba, kofofin Kudus za su isa kofofin Damascus'.