Isra'ila ta kwashe kwana 262 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,598 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,032, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 0120 GMT — Isra'ila ta shirya gwabza yaƙi daban-daban — Netanyahu Isra'ila tana shirin sauya lamura a kan iyakarsa da Lebanon amma tana fatan ba za ta buƙaci yin hakan ba, in ji Firaminista Benjamin Netanyahu, yayin da yake magana game da fafatawar da sojojinsu suke yi da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon. Da yake hira da gidan talbijin na Channel 14 game da yiwuwar tsunduma yaƙi gadan-gadan da Hezbollah, Netanyahu ya ce idan buƙatar hakan ta taso, “za mu fuskanci wannan ƙalubalen shi ma. Za mu iya yin yaƙi daban-daban. Mun shiryawa hakan.” Game da yaƙin Gaza, ya ce sun kusa kawo ƙarshen hare-hare masu tsanani, amma ba za su daina yaƙi ba sai sun ƙwace ikon yankin daga hannun Hamas. Netanyahu ya ce Tel Aviv na son kafa wasu “ƙabilu 'yan ƙasa” domin gudanar da mulki a Gaza. Kazalika ba zai "yiwu" Isra'ila ta sake kafa matsugunan 'yan-kama-wuri-zauna a Gaza. 0200 GMT — Bama-bamai da Isra'ila ta harba a Birnin Gaza sun kashe ma'aikatan lafiya biyu Falasɗinawa biyu da ke aiki da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza sun mutu sannan da dama sun jikkata sakamakon wasu hare-haren bama-bamai ta sama da Isra'ila ta kai a wani ƙaramin asibiti a Birnin Gaza. Rundunar 'yan bijilanti ta Gaza ta bayyana haka a wata sanarwa tana mai cewa “tawagarmu ta gano gawa guda biyu ta ma'aikatan lafiya da suka yi shahada sannan da dama sun jikkata yayin da jirgin sojojin mamaya ya kai hari a ƙaramin asibiti na Al Daraj,” ko da yake ba ta yi ƙarin bayani ba. 0021 GMT — Isra'ilawa sun jikkata a harin makamai masu linzami da aka kai musu daga kudancin Lebanon Isra'ilawa biyu sun jikkata yayin da wasu makamai masu linzami da aka harba daga Lebanon suka faɗa wani gida. “Mutum biyu sun samu rauni ba mai tsanani ba” sakamakon makamai masu linzami da aka harba waɗanda suka nufi birnin Metula na arewacin Isra'ila, a cewar gidan rediyon rundunar sojojin Isra'ila a saƙon da ya wallafa a shafin X. Rahotanni sun ce wani helikwafta ya kwashe mutanen da suka jikkata inda ya kai su Cibiyar Lafiya ta Rambam da ke Haifa. Hukumomin Lebanon ba su ce komai kan batun ba.
Архив новостей
В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.
Kai-tsaye: Isra'ila ta shirya gwabza yaƙi daban-daban — Netanyahu
Isra'ila ta kwashe kwana 262 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,598 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,032, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 0120 GMT — Isra'ila ta shirya gwabza yaƙi daban-d...

Кратко
Isra'ila ta kwashe kwana 262 tana kai hare-hare a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 37,598 — galibinsu jarirai, mata da yara — ta jikkata sama da mutum 86,032, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine, kana ta sace mutum 9,500. 0120 GMT — Isra'ila ta shirya gwabza yaƙi daban-d...
