الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Younis

Tsawon kwanaki 137, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,092 da raunata mutum 69,028. 0753 GMT — Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Yo...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
KAI-TSAYE: Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Younis
لمحة سريعة

Tsawon kwanaki 137, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,092 da raunata mutum 69,028. 0753 GMT — Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Yo...

Tsawon kwanaki 137, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 29,092 da raunata mutum 69,028. 0753 GMT — Isra'ila ta sanar da mutuwar wani sojanta da aka raunata a Khan Younis Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar da mutuwar ƙarin sojinta ɗaya wanda ya samu rauni a yayin wata arangama da Falasɗinwa a kudancin Zirin Gaza. A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta bayyana cewa sojan da ya mutu Staff Sgt. Maoz Morell mai shekara 22, ya samu mummunan rauni a ranar 15 ga watan Fabrarairu a yayin wata arangama da Falasɗinawa wadda ta yi sanadin mutuwar sojin Isra’ila ɗaya da raunata takwas. Aƙalla sojojin Isra’ila 236 aka kashe a Gaza tun bayan da Isra’ila ta soma kai hari ta ƙasa a Gaza a ranar 27 ga watan Oktoba, sai dai jimlar adadin sojin da aka kashe tun bayan soma rikicin a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 575.