Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 118 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,019 sannan suka jikkata mutum 66,139, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1356 GMT — Isra'ila ta saki Falasdinawa 114, mafi yawansu sun samu karaya Hukumomin Isra'ila sun saki Falasdinawa 114 da suka hada da mata hudu da sojojin Isra'ila suka tsare a lokacin farmakin da suka kai a Zirin Gaza a baya-bayan nan. Wani jami'in Falasdinawa da ke kula da mashigar Gaza ya bayyana cewa, an sako Falasdinawan ta hanyar mashigar kasuwanci ta Karem Abu Salem, wacce aka fi sani da Mashigar Kerem Shalom, a kudancin Gaza. An kai goma daga cikin mutanen da aka sako ciki har da wata mata zuwa asibiti a birnin Rafah saboda yanayin lafiya. Wata majiyar lafiya ta ce sun sami karaya mai muni musamman a hannayensu da kafafunsu, sakamakon dukan da sojojin Isra'ila suka yi musu a hannunsu. Wasu sun samu toshewar jini a wuyansu da kawunansu, yayin da wasu kuma ke fama da wahalar numfashi da raunuka da sagewa da kumburin hannayensu, in ji majiyar. 0215 GMT — Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kisan da ake yi da kuma rufe bakin 'yan jarida a Gaza Kwararru kan kare hakkin Majalisar Dinkin Duniya sun yi kakkausar suka kan karuwar 'yan jaridun da ake kashewa a Gaza, suna masu yin Allah wadai da wata dabarar "da gangan" da Isra'ila take yi na rufe bakin masu aika rahotanni. "Da wuya a ga wani yanayi da ake kashe 'yan jarida sosai saboda kawai suna gudanar da aikinsu kamar yadda yake faruwa a Gaza a yanzu," in ji kwararrun biyar a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Rahotannin da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na nuni da cewa akalla ‘yan jarida 122 da wasu ma’aikatan yada labarai ne aka kashe tare da jikkata wasu da dama a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza. Masanan sun ce "Mun firgita da yawan 'yan jarida da ma'aikatan yada labarai da aka kashe, aka kai musu hari, aka raunata su da tsare su a yankin Falasdinawa da aka mamaye, musamman a Gaza, a cikin 'yan watannin nan." 1049 GMT — Yawan mutanen da aka kashe a Gaza sun wuce 27,000 Akalla mutum 27,019 ne suka mutu a cikin kusan watanni hudu na yakin da Isra'ila take yi a Gaza, in ji Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya. / Photo: AA Akalla mutum 27,019 ne suka mutu a cikin kusan watanni hudu na yakin da Isra'ila take yi a Gaza, in ji Ma'aikatar Lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya. Wata sanarwar ma'aikatar ta kuma ce an jikkata mutum 66,139 tun bayan ɓarkewar yaƙin na Gaza ranar 7 ga watan Oktoban 2023, 0744 GMT — Isra'ila ta kama gomman Falasɗinawa a Gabar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun raunata wasu Falasdinawa biyu tare da kame akalla wasu 37 yayin wani jerin sabbin kutse da suka yi a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye, a cewar majiyoyin lafiya. Majiyoyin lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an harbi Falasɗinawa a yayin da ake arangama da sojojin Isra'ila a birnin Tubas da ke arewaci. An harbi daya daga cikinsu a gadon baya daya kuma a kafa. A cewar majiyoyin lafiya, dakarun Isra'ila sun dirar wa Tubas tare da kama Falasɗinawa biyu, lamarin da ya jawo yin arangama da gomman Falasɗinawa. Sojojin Isra'ila sun yi amfani da harsasai da kuma barkonon tsohuwa, wajen tarwatsa Falasdinawan da ke jifan dakarunsu da duwatsu, kamar yadda majiyar ta bayyana.
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta saki Falasdinawa 114, mafi yawansu sun samu karaya
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 118 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,019 sannan suka jikkata mutum 66,139, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1356 GMT — Isra'ila ta saki Falasdinawa 114, mafi yawansu sun samu karaya Hukumom...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 118 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 27,019 sannan suka jikkata mutum 66,139, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 1356 GMT — Isra'ila ta saki Falasdinawa 114, mafi yawansu sun samu karaya Hukumom...
