Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Isra'ila ta sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da ta kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 2011 GMT — Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙ...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da ta kai Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Bu haberde ne var?

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 2011 GMT — Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙ...

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na 32 a yau — bayan yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a yankin ya kashe Falasɗinawa fiye da 48,291, ko da yake daga baya an tabbatar mutanen sun kusa 62,000. Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025 2011 GMT — Dakarun Isra'ila sun sace Falasɗinawa aƙalla 30 a samamen da suka kai wasu yankuna a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar kamfanin dillancin labaran WAFA. Dakarun na Isra'ila sun tafi da Falasɗinawa shida a yankin Ramallah da al Bireh, a cewar kamfanin labaran. Kazalika sun tafi da Falasɗinawa huɗu daga Jenin, ciki har da ƙananan yara biyu, kana sun ɗauke mutane uku a yankin Qalqiliya. Ƙarin labarai ???? 0248 GMT — Lebanon ta gano gawawwakin mutane 23 bayan dakarun Isra'ila sun janye daga kudancin ƙasar Rundunar tsaron fararen-hula ta Lebanon ta ce ta gano gawawwakin mutane 23 a wasu garuruwa da ke kudancin ƙasar bayan dakarun Isra'ila sun janye daga yakunan sakamakon yarjejniyar tsagaita wuta da aka amince da ita. A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce tawagarta da ke kai ɗauki, wadda ke aiki da dakarun rundunar sojin Lebanon, ta gudanar da bincike a yankunan da lIsra'ila ta kai was hare-hare inda ta gano gawawwakin mutanen. Tawagar ta ce ta gano gawawwakin mutum 14 a garin Meiss El Jabal, da gawwaki uku a garin Markaba, da gawawwaki uku a Kfarkela da kuma gawawwaki uku a Odaisseh.