Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙona Falasɗinawa 4 da ransu a harin da ta kai tantunan 'yan gudun hijira

Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 0322 GMT — Falasɗin...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta ƙona Falasɗinawa 4 da ransu a harin da ta kai tantunan 'yan gudun hijira
En bref

Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 0322 GMT — Falasɗin...

Yaƙin da mahukuntan Tel Aviv suka kwashe shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,227. A gefe guda, hare-haren da Isra'ila ta ƙadamar a Lebanon tun Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,306 da raba miliyan 1.2 da muhallansu. Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 0322 GMT — Falasɗinawa aƙalla huɗu ne Isra'ila ta ƙona da ransu, tare da jikkata mutum fiye da 40 a wani hari da ta kai a tantuna da wasu fararen-hula da aka kora daga gidajensu suke samun mafaka a Gaza, a cear kafofi watsa labaran yankin. Gobara ta tashi a tantunan da ke jikin Asibitin al-Aqsa Martyrs, wanda ke birnin Deir al Balah, sakamakon harin, a cewar kamfanin dillanacin labaran Falasɗinu WAFA. Hotuna da bidiyoyin da aka riƙa watsawa a shafukan intanet sun nuna yadda mutane suka makale a cikin tantunan sannan hayaƙi ya turnuƙe su. 2316 GMT —Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin da Isra'ila ta kai a wata makaranta a Gaza ya ƙaru zuwa 22 Adadin mutanen da suka mutu sakamakon wani hari ta sama da Isra'ila ta kai a wata makaranta a tsakiyar Gaza ya ƙaru zuwa 22, a cewar ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin. Ya ƙara da cewar sojojin Isra'ila "suna sane cewa dubban mata da yara da aka kora daga gidajensu suna samun mafaka a makarantar ta Mufti amma suka kai mata hari da bama-bamai." Falasɗinawa suna yin sallar jana'iza ga wasu 'yan'uwansu da aka kai Asibitin Nasser bayan kisan da Isra'ila ta yi musu a harin da ta kai birnin Rafah / Hoto: AA Ƙarin bayani ???? 0212 GMT — Amurka ta nemi Isra'ila a bi hanyar diflomasiyya kan yaƙin Lebanon Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin ya ce akwai buƙtatar Isra'ila ta daina amfani da ƙarfin soji kana ta rungumi hanyar diflomasiyya a yaƙin da take yi a Lebanon. Da yake magana ta wayar tarho da Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant, Austin ya ce ya ika ta'aziyyarsa bisa mutuwar sojojin Isra'ila a wani hari na jirgi mara matuƙi da Hezbollah ta kai musu. "Na jaddada buƙatar tabbatar da tsaron lafiyar (Dakarun Wanzar da Tsaro na MDD a Lebanon) UNIFIL da Sojojin Lebanon da kuma buƙatar mayar da hankali kan sulhu ta hanyar diflomasiyya da daina amfani da ƙarfin soji," in ji shi a saƙn da ya wallafa a shafin X. 2142 GMT — Isra'ila ta ce harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi ya kashe sojojinta 4 Rundunar sojojin Isra'ila ta ce sojojinta huɗu sun mutu sakamakon harin da Hezbollah ta kai da jirgi mara matuƙi a sansaninsu da ke kudancin Haifa. "An kashe sojoji huɗu na IDF a harin, sannan guda bakwai sun yi mummunar jikkata,"a cewar wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar.