Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 339, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Litinin, 9 ga Satumban 2024 0125 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai farmaki a garin Tulkarem da sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan. Dakarun mamaya na Isra'ila sun mamaye Tulkarem bayan tsakar dare, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinawa Wafa ya bayyana. Rahoton ya kara da cewa, wasu motocin sojojin mamaya tare da rakiyar manyan buldoza guda biyu sun shiga birnin daga bangarensa na yammacin kasar, inda suka fara rusa ababen more rayuwa a yankin Al-Alemi, yayin da wani jirgin sama mara matuki na sa ido ya yi ta shawagi ta saman birnin. Wafa ya kuma ruwaito cewa, sojojin Isra'ila sun kai farmaki sansanin 'yan gudun hijira na Balata da ke gabashin Nablus tare da rakiyar buldoza ta soji, lamarin da ya kai ga arangama da dakarun gwagwarmayar Falasdinawa. Shaidun gani da ido sun ce an yi arangama tsakanin Falasdinawa da sojoji a kofar shiga sansanin. Masu fafutuka sun yada bidiyon da ke nuna motocin soji da kuma buldoza yayin farmakin. 0136 GMT — Majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta yi taro don magance tashe-tashen hankula a Gabar Yammacin Kogin Jordan Ma'aikatar tsaron Isra'ila karkashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu, ta yi taro domin tattauna muhimman batutuwa da dama, musamman tabarbarewar yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da ta mamaye, kamar yadda hukumar yada labaran kasar ta sanar. Hukumar ta yi nuni da cewa Netanyahu ya bude zaman, inda aka tattauna batutuwa da dama, tare da mai da hankali kan yadda al'amura ke kara tabarbarewa a yankin Falasdinu da aka mamaye. Yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a Gaza, sojojin Isra'ila sun fadada ayyukansu tare da kara kai hare-hare a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 692 tare da jikkata wasu kimanin 5,700, baya ga wadanda aka kama a cewar majiyoyin hukumomin Falasdinu. A yayin ganawar, Netanyahu ya kuma tabo ziyarar da ministocin gwamnati ke yawan kaiwa Masallacin Ƙudus.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kutsa kai cikin sansanonin Falasdinawa, inda rikici ya ɓarke da mazauna yankin
Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 339, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Litinin, 9 ga Satumban 2024 0125 GMT — Sojojin Isra'ila su...

لمحة سريعة
Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga rana ta 339, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,000 – yanwacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,000, kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. Litinin, 9 ga Satumban 2024 0125 GMT — Sojojin Isra'ila su...
