Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0700 GMT — Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da mata biyu da yara biyar Isra'la ta kashe a wani sabon hari ta sama da ta kai wata makaranta ɗauke da farar hula a tsakiyar Gaza. An kashe wata uwa da 'ya'yanta huɗu haka kuma an jikkata wasu a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai gidan iyalin Al-Samak da ke birnin Deir al Balah, kamar yadda hukumar kare farar hula ta Gaza ta tabbatar. A wata sanarwa ta daban, hukumar kare farar hulan ta kara da cewa harin da Isra'ila ta kai kan makarantar Khaled Bin Al-Waleed da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, ya kashe wani mutum, matarsa, da 'yarsu, tare da jikkata wasu. 0630 GMT — Gomman hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama a kudanci da gabashin Lebanon sun yi sanadin mutuwar aƙalla farar hula ɗaya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na NNA ya tabbatar. “Jiragen yaƙin maƙiya sun ƙaddamar da hare-hare....sama da hare-hare 80 a cikin minti 30”, inda suka afka gundumar Nabatiyeh da ke kudancin Lebanon,” in ji kamfanin dillancin labaran na Lebanon. Wannan harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare tsakanin mayaƙan Hezbollah na Lebanon da kuma sojojin Isra’ila.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe yara biyar da mata biyu a wani sabon harin da ta kai Gaza
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0700 GMT — Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da ma...

At a glance
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga rana ta 353, inda ta kashe kusan Falasɗinawa 41,431 – yawacinsu mata da yara – tare da jikkata kusan 95,818 kuma wani ƙiyasi ya nuna cewa fiye da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-ginen da aka rusa. 0700 GMT — Aƙalla Falasɗinawa takwas waɗanda suka haɗa da ma...
