Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na goma — bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 47,306. A gefe guda, UNRWA na shirin daina aiki a Gabashin Ƙudus, sannan dakarun Tel Aviv na kai hari kan Falasɗinawa da ke komawa arewacin Gaza. Talata, 28 ga Janairu, 2025 2023 GMT — Isra'ila ta kashe wata yarinya Bafalasɗiniya tare da jikkaTA mutum uku a hari ta sama da dakarunta suka kai kan Falasɗinawa 'yan gudun hijira da ke kan hanyar al Rashid domin komawa Gaza. Asibitin Al Awda da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat a tsakiyar Gaza ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da kisan, yana mai cewa: "Wata yarinya Bafalasɗiniya ta yi shahada, yayin da mutum uku suka jikkata sakamakon hari ta sama da Isra'ila ta kai wa Falasɗinawa 'yan gudun hijira da ke bin hanyar al Rashid domin komawa arewacin Gaza." Ƙarin labarai???? 2316 GMT — Rubio ya tattauna da Sarki Abdullah na Jordan kan yarjejejiyar tsagaita wuta a Gaza Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi wayar tarho da Abdullah na Jordan, kwanaki kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da shawarar kwashe Falasɗinawan da ke Gaza zuwa ƙasashen Jordan da Masar . "Sakataren Harkokin Wajen Amurka da Sarki Abdullah sun tattauna kan aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, da samar da wata hanya ta tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin," in ji wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar. Sai dai sanarwar ba ta ambaci shawarar da Trump ya bayar ba.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe wata yarinya Bafalasɗiniya, ta jikkata mutum 3 da ke kan hanyar komawa Arewacin Gaza
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na goma — bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 47,306. A gefe guda, UNRWA na shirin daina aiki a Gabashin Ƙudus, sannan dakarun Tel Aviv na kai hari kan Falasɗinawa da ke komawa arewacin Gaza. Talata, 28 ga Janairu, 2025 2023 GMT — Isra'ila...

لمحة سريعة
Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta shiga kwana na goma — bayan Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 47,306. A gefe guda, UNRWA na shirin daina aiki a Gabashin Ƙudus, sannan dakarun Tel Aviv na kai hari kan Falasɗinawa da ke komawa arewacin Gaza. Talata, 28 ga Janairu, 2025 2023 GMT — Isra'ila...
