Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 328, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,534 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,778, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024 0849 GMT — Isra'ila ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
De un vistazo

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 328, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,534 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,778, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024 0849 GMT — Isra'ila ta...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 328, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,534 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,778, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Alhamis, 29 ga watan Agusta, 2024 0849 GMT — Isra'ila ta kashe wani kwamandan ƙungiyar Islamic Jihad a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad ta sanar da mutuwar kwamandanta a sansanin 'yan gudun hijira na Nur Shams da ke yankin Tulkarem na Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye. Da farko, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da kashe mayaƙa 'yan gwagwarmaya biyar, ciki ar da Muhammad Jabber, wanda aka fi sani da Abu Shujaa. "Abu Shujaa, kwamandan Rundunar Tulkarem Brigade da ke ƙarƙashin Rundunar Al-Quds," wato ɓangaren gwagwarmaya na Islamic Jihad, da ke da ƙarfi a sansanonin 'yan gudun hijira a arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, "ya mutu ne tare da 'yan'uwa da dama na rundunar bayan sun gwabza faɗa da sojojin Isra'ila masu mamaya", a cewar sanarwar da ƙungiyar ta fitar. 2000 GMT — 'Yan jam'iyyun adawar Isra'ila sun amince su kawar da Netanyahu a yayin da yake ci gaba da kai hare-hare a Gaza Shugaban 'yan Dimokuraɗiyya Yair Golan ya yi kira ga shugabannin jam'iyyun adawa a Isra'ila su gudanar da taron gaggawa domin kawar da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu. Wani saƙon murya da Golan ya wallafa a shafinsa na X ya ce, "A yau, na tuntuɓi dukkan abokaina a jam'iyyun adawa inda na gaya musu saƙona ƙarara cewa ya kamata mu kama hanya iri ɗaya." Ya ƙara da cewa, "Isra'ila tana cikin mawuyacin hali kuma tana durƙushewa a fannin siyasa da fannin tattalin arziki da mu'amala da kundin tsarin mulki. "Komai yana wargajewa a idanunmu. Dole mu yi aiki tare kuma cikin tsanaki tare da jajircewa." Golan ya wallafa saƙon da ya tura wa shugabannin jam'iyyun adawa, da ke cewa: "Muna tsaka da yaƙi, inda aka kwashe kwana 328 ana garkuwa da mutanenmu, kana an raba dubban mutane da gidajensu, sannan tattalin arzikinmu yana durƙushewa, kuma sojojinmu sun kwashe tsawon lokaci suna yaƙi ba tare da samu mafita ba. "Rashin amincewa da gwamnati da kuma matakan da take yin gaban kanta wajen ɗaukarsu bisa muradunta na siyasa su suka tilasta mana yin wannan yunƙuri." Da yake yin martani ga saƙon Golan, shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i." Shugaban jam'iyyun adawa a Isra'ila Yair Lapid ya wallafa saƙo a shafinsa na X da ke cewa, "Za mu ci gaba da yin aiki da dukkan 'yan adawa, a fili da kuma a bayan-fage, har sai mun kawar da wannan gwamnati da ta jefa ƙasarmu cikin bala'i." / Hoto: Reuters