Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 218, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,943 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,572 ne suka jikkata. 1043 GMT — Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa An kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu a wani hari ta sama da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labarai na gwamnati ya sanar a Gaza. An kashe ɗan jarida Bahaa Okasha, wanda mai ɗaukar hoto na Al-Aqsa media network, tare da matarsa da ɗansa a wani harin ba da Isra’ila ta kai kan gidansa da ke sansanin gudun hijira na Jabalia. Aƙalla ƴan jarida 143 ne Isra’ila ta kashe a yaƙin da take yi a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa sama da 35,000 tun daga 7 ga watan Oktoba. 0947 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan sojojin Isra'ila da ke kan iyaka Kungiyar Hezbollah a ranar Asabar ta ce ta kai hari kan wani gini wanda sojojin Isra'ila suka taru a kusa da iyakar Lebanon da ke kudancin ƙasar. A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce mayaƙanta sun kai hari kai tsaye kan "wani gini wanda sojoji suke a Metula da makamai masu kyai. Harin ya kasance "a matsayin martani ga hare-haren da masu tsatsauran ra'ayin Yahudawa suka kai kan ƙauyukan kudanci da gidajen fararen hula, wanda na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai a garin Tayr Harfa," in ji Hezbollah, yayin da ƙungiyar ke magana kan harin na ranar Juma'a wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutane biyu.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 218, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,943 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,572 ne suka jikkata. 1043 GMT — Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa An kashe wani ɗan jarida...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 218, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,943 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,572 ne suka jikkata. 1043 GMT — Isra'ila ta kashe wani ɗan jaridar Falasɗinu da iyalansa An kashe wani ɗan jarida...
