Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 161 - ya kashe aƙalla mutane 31,341, galibi yara da mata, tare da jikkata 73,134. 2200 GMT — Isra'ila ta kashe tare da raunata mutane da 'dama' da ke jiran agajin abinci a Gaza Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta ce Isra'ila ta kai hari kan Falasdinawa da ke jiran agajin jinƙai a zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, lamarin da ya yi sanadiyar kashe tare da jikkata wasu da dama. Ta kuma kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya ƙaruwa yayin da aka kai gawarwaki akalla 21 da wasu fiye da 155 da suka jikkata zuwa asibitoci. A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce Falasdinawa na jiran agajin jinƙai a mashigin Gaza na Kuwaiti, inda ta ce tana nuna shirin da Isra'ila ta yi na aiwatar da wani sabon kisan kiyashi mai ban tsoro. Hukumar ta ce ana ci gaba da aikin kwashe wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata duk da kalubalen da yankin ke fuskanta. Sanarwar ta kara da cewa adadin wadanda suka mutu na iya karuwa saboda mummunan yanayin da wadanda suka jikkata ke ciki, wadanda ake kula da su a asibitocin da ke kusa. Kamfanin dillancin labaran kasar Falasdinu WAFA ya tabbatar da cewa an kashe mutane da dama tare da jikkata wasu. Sojojin Isra'ila kamar yadda suka saba sun nisantar da kansu daga sabon kisan gillar na Gaza, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce sojojinta da suka mamaye yankin ba su yi luguden wuta kan Falasdinawa da ke jiran agaji ba. Mohammed Ghurab, daraktan bayar da agajin gaggawa a wani asibiti a arewacin Gaza, ya shaida wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa, sojojin sun buɗe wuta kai tsaye a kan mutanen da suka taru a zagayen dajin domin jiran wata motar abinci. Wani dan jarida na AFP da ke wurin ya ga gawarwaki da kuma mutanen da aka harbe. 2143 GMT — Ofishin Netanyahu ya ce sabon matakin sasantawa da Hamas har yanzu ba shi da tabbas Ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce wata sabuwar shawara da kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta gabatar ga masu shiga tsakani ba ta kan tsarin da ya dace. Sanarwar ta ce a ranar Juma'a za a gabatar da cikakken bayani kan batun ga majalisar ministocin yaƙin da tsawaita wa'adin tsaro.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe tare da raunata mutane da 'dama' da ke jiran agajin abinci a Gaza
Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 161 - ya kashe aƙalla mutane 31,341, galibi yara da mata, tare da jikkata 73,134. 2200 GMT — Isra'ila ta kashe tare da raunata mutane da 'dama' da ke jiran agajin abinci a Gaza Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza t...

A taƙaice
Yakin da Isra'ila ke yi a kan Falasɗinawa da ke Gaza - wanda ke cikin kwanaki na 161 - ya kashe aƙalla mutane 31,341, galibi yara da mata, tare da jikkata 73,134. 2200 GMT — Isra'ila ta kashe tare da raunata mutane da 'dama' da ke jiran agajin abinci a Gaza Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza t...
