Gida / Taskar labarai
Taskar labarai

Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe shugabanni uku na Falasɗinawa a harin da ta kai tsakiyar Beirut

A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0644 GMT — Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare...

NewstimeTR Haber Merkezi · · An sabunta 2026-08-13, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe shugabanni uku na Falasɗinawa a harin da ta kai tsakiyar Beirut
A taƙaice

A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0644 GMT — Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare...

A yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 360, ta kashe Falasɗinawa fiye da 41,595. Kazalika, ta kashe fiye da mutum 800 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon ranar 23 ga watan Satumba. Litinin, 30 ga watan Satumba, 2024 0644 GMT — Dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da sanyin safiyar Litinin a yankin Kola na birnin Beirut, wanda ya kasance irinsa na farko da suka kai a cikin babban birnin na Lebanon tun da suka soma yaƙi da Hezbollah a watan Oktoban da ya wuce. Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito cewa jirgi mara matuƙi na Isra'ila ya kai hari a hawa na biyar na wani gida a kan hanyar da ta haɗa Beirut da Filin Jirin Saman Ƙasa da Ƙasa na Rafik Hariri. Harin ya tayar da gobara a gidan, ko da yake 'yan kwana-kwana sun kashe ta. Daga bisani ƙungiyar Popular Front for the Liberation of Palestine (PFLP) ta tabbatar da cewa harin ya kashe shugabanninta uku: Mohammed Abdel Aal, wani mamba na ɓangaren siyasarta kuma shugaban sashen soja da tsaro; Imad Ouda, kwamanda soji na Lebanon, da Abdel Rahman Abdel Aal, wanda ba a bayyana matsayinsa ba. 0554 GMT — Hamas ta tabbatar da kisan shugabanta a harin Isra'ila Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinawa, Hamas, ta ce an kashe shugabanta na Lebanon Fateh Sherif Abu el-Amin tare da iyalansa a wani hari da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar.