Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah

Tsawon kwanaki 129, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,340 da raunata mutum 67,984. 1053 GMT — Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah Sama da mutum 10...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah
Kwa muhtasari

Tsawon kwanaki 129, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,340 da raunata mutum 67,984. 1053 GMT — Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah Sama da mutum 10...

Tsawon kwanaki 129, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 28,340 da raunata mutum 67,984. 1053 GMT — Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 100 a Rafah Sama da mutum 100 Isra'ila ta kashe a hare-haren da ta kai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito. Birnin na Rafah na daidai iyakar ta Gaza da Masar, wanda wuri ne wanda sojojin Isra'ila suka tilasta wa farar hula gudun hijira inda suke inda suka yi iƙirarin cewa wuri ne mai aminci. Sojojin Isra'ila a ranar Lahadi sun amince da a kai hari ta ƙasa a Rafah. Falasdinawa sun nemi mafaka a Rafah a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a sassan Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.