Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe mutum 90 a arewacin Gaza cikin awa 24

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 413 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,056 tare da jikkata fiye da mutum 104,268. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,583 tare da jikkata 15,000 tun daga watan Oktoban 2023. Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024 2203 GMT — Jirag...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe mutum 90 a arewacin Gaza cikin awa 24
At a glance

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 413 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,056 tare da jikkata fiye da mutum 104,268. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,583 tare da jikkata 15,000 tun daga watan Oktoban 2023. Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024 2203 GMT — Jirag...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 413 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,056 tare da jikkata fiye da mutum 104,268. A Lebanon, Isra'ila ta kashe fiye da mutum 3,583 tare da jikkata 15,000 tun daga watan Oktoban 2023. Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024 2203 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla biyu tare da jikkata gommai yayin da suka yi luguden wuta a arewacin Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe tun daga safiyar Alhamis zuwa yanzu ya kai mutum 90, a cewar likitoci. Isra'ila ta kai hari a gidan iyalan Al-Dayah da ke yankin Al-Sabra da kudancin Birnin Gaza, in ji kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA , inda ya ƙara da cewa ma'aikatan agaji da motocin ɗaukar marasa lafiya suna can suna lalubo mutanen da ɓuraguzai suka danne. Kazalika an jikkata ma'aikatan asibiti Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka, sakamakon bama-baman da jiragen Isra'ila marasa matuƙa suka jefa a harabar asibitin. Wani ma'aikacin asibitin ya ce jiragen sun harba bama-bamai a kan janareton da ke bayar da wuta ga ɗaukacin asibitin inda suka lalata shi. 2346 GMT — Biden ya ce sammacin da Kotun ICC ta bayar na kama Netanyahu 'abin takaci ne' Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana matakin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na neman kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa a matsayin "abin takaici". "Sammacin da ICC ta bayar na kama shugabannin Isra'ila abin takaici ne," in ji Biden a wata sanarwa da ya fitar. "Bari na sake bayyanawa ƙarara cewa: duk abin da ICC za ta nuna, ba za a haɗa Isra'ila da Hamas ba. Za mu kare Isra'ila daga duk wata barazana ga tsaronta daga kowa."