Accueil / Archives
Archives

Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaza — Jami'ai

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 07:30 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaz...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Mis à jour 13/08/2026 05:26:13
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaza — Jami'ai
En bref

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 07:30 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaz...

Wannan shafi ya kawo muku sabbin bayanai a ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra'ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba. 07:30 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya kusan 100 a Gaza — Jami'ai Kungiyar Bayar da Agaji ga Falasdinawa 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ta ce an kashe ma'aikatanta 99 tun lokacin da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba. Kwamishina Janar na UNRWA Philippe Lazzarini ne ya bayyana haka a wurin taron Kasashen Duniya Don Samar Da Jinkai ga Fararen-Hulan Gaza da aka yi a Paris, babban birnin Faransa. "Wata daya da ya gabata ya kasance mai matukar wahala ga UNRWA," in ji Lazzarini. Ya ce "an kashe abokan aikina 99 maza da mata a Gaza. Wannan shi ne adadi mafi girma na ma'aikatan kungiyar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da aka kashe sakamakon rikici a kankanen lokaci." 05:30 GMT — Yakin Isra'ila a Gaza ya jefa Falasdinawan Gaza 'sama da 400,000' cikin talauci Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana yadda tattalin arzikin Falasdinu yake rushewa bayan Israila ta kwashe fiye da wata daya tana yi wa Gaza luguden wuta tare da yi wa daukacin yakin kawanya. Tattalin arzikin Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza ya fadi da kashi hudu cikin dari lamarin da ya jefa fiye da mutum 400,000 cikin talauci — abin da ba a taba gani ba a yakin Syria da na Ukraine, da ma yake-yaken da aka yi tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na yankin Gaza a baya. Isra'ila ta lalata ko ta rusa akalla kashi 45 cikin dari na dukkan gidajen Gaza, a cewar wata kididdiga da Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Ci-gaba UN Development Program da kuma na Tattali Arziki da Walwala a Yankin Asiya wato UN Economic and Social Commission for West Asia suka fitar. 'Yan uwan Al Kurd, wanda Isra'ila ta kashe, a yayin da suke alhinin rasuwarsa bayan dauko gawarsa daga Asibitin Al Aqsa na Deir Al Balah, Gaza ranar 20 ga watan Oktoba, 2023. / Hoto: AA