Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi — hukumomi

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0727 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi Akalla...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi — hukumomi
At a glance

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0727 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi Akalla...

Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 220, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 35,034 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,755 ne suka jikkata. 0727 GMT — Isra'ila ta kashe ma'aikatan lafiya sama da 500 a Gaza tun bayan soma yaƙi Akalla ma'aikatan kiwon lafiya 500 ne aka kashe tun farkon yakin da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta bayyana a daidai lokacin da ake bikin ranar ma’aikatan jinya ta duniya. Ma’aikatar ta lafiya ta bayyana cewa sojojin na Isra’ila sun kashe malaman jinya 138 a wannan yaƙi. Sannan akwai wasu ma’aikatan lafiyan 1500 da aka jikkata da kuma kama 312. 0630 GMT — Sojojin Isra'ila sun ce sun kai hari kan wurare uku na Hezbollah a kudancin Lebanon Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa jiragen yakinta sun kai hari kan wasu wurare uku na kungiyar Hizbullah a kudancin kasar Lebanon. “Jiragen sojin sama sun yi ruwan bama-bamai a wasu wuraren harba makamai masu linzami na Hezbollah a kauyukan Helta da Al-Hamam da kuma lalata ababen more rayuwa mallakar kungiyar a yankin Khraibeh. Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Hezbollah ta ce ta kai hari da wasu sabbin makamai masu linzami a kan wani wurin ajiye sojojin Isra'ila a kusa da yankin Zabdine a cikin gonakin Shebaa na Lebanon da suka mamaye.