Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 27i tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,925 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,141 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0330 GMT — Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-hare a Birnin Gaza, inda ta kashe gomman Falasɗinawa fararen hula, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa WAFA ya bayyana, inda yace an samu rahotannin jikkata mutane daga yankunan Sheikh Radwan da Shujaeya da kuma gabashin Birnin Gaza. Tun da farko, Isra’il ta kashe aƙalla fararen hula 12, ta kuma jikkata wasu a hare-haren jiragen sama a Deir al Balah a tsakiyar Gaza da aka mamaye, kamar yadda WAFA ya rawaito. Wakilin WAFA ya ce an kai gawawwakin mutane 12 Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al Balah bayan hare-haren sama kan gidan iyalen Eslayyim a birnin. Isra’ila ta kuma kashen wasu fararen hular uku a yankin Al-Mansura a unguwar Shejaiya, da wasu ukun kuma daban a yammacin Rafah, a cewar kamfanin dillnacin labaran. Hukumomin lafiya sun shaida wa WAFA cewa daga wayewar gari an kai aƙalla gawawwakin fararen hula 31 asibitocin yankin.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe gomman Falasɗinawa a hare-haren da ta kai Zirin Gaza
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 27i tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 37,925 — galibinsu mata da yara –– sannan kimanin mutum 87,141 sun jikkata, kana fiye da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai kuma Isra'ila ta sace kusan mutum 9,500. 0330 GMT — Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-har...