Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis

Tsawon kwanaki 106, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,762 da raunata mutum 62,108. 0902 GMT — Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis Isra’ila...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis
De un vistazo

Tsawon kwanaki 106, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,762 da raunata mutum 62,108. 0902 GMT — Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis Isra’ila...

Tsawon kwanaki 106, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 24,762 da raunata mutum 62,108. 0902 GMT — Isra'ila ta kashe farar hula bakwai a Gaza da Khan Younis Isra’ila ta kashe farar hula akalla bakwai a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma unguwar Al Amal da ke Khan Younis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya ruwaito. Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari wani gida mallakar iyalan Darwish a sansanin, wanda hakan ya jawo kisan farar hula biyar a sansanin da kuma raunata wasu da dama. Haka kuma jiragen yakin na Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama a unguwar Al Amal inda suka kashe akalla mutum biyu da kuma raunata wasu da dama.