Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu
Кратко

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 162 tana kai wa Falasɗinawan da ke Gaza sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 31,490 tare da jikkata mutum fiye da 73,439 a yayin da Netanyahu ya amince da shirin mamaye Rafah duk da Allah wadai da duniya ke yi. 0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fararen-hula 80 a sabbin hare-hare da ta kai Gaza — Falasɗinu Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 80 sannan suka jikkata a wasu hare-haren tsakar dare da suka kai a gidaje da wasu gine-gine a Gaza, a cewar kafofin watsa labaran Falasɗinu da hukumomi. Kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa (WAFA) ya ce Isra'ila tana ci gaba da kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa a yankuna daban-daban, ciki har da sansanin ƴan gudun hijira na Nusairat da Birnin Gaza. Sojoji sun jefa bama-bamai a gidajen da ke Titin Al Jala, inda ɓaraguzan gine-gine suka danne jama'a. Sun rusa wani gini mai hawa bakwai kusa da Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza, inda Falasɗinawan da suka rasa gidajensu suke samun mafaka, abin da ya kai ga mutuwar gomman mutane da jikkatar wasu. Ma'aikatan agaji sun zaƙulo gawawwaki biyar na Falasɗinawa daga ɓaraguzan gine-gine, yayin da ake ci gaba da aikin ceto. 0115 GMT — Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mata masu ciki da ƙananan yara 36 a sabbin hare-haren da suka kai Gaza Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hare-hare a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa fararen-hula aƙalla 36, gaibinsu ƙananan yara da mata masu ciki, a cewar wata sanar da hukumomn Falasɗinu suka fitar. "Sojojin mamaya na Isra'ila sun kai harin bama-bamai a gidan iyalan al Tabatibi da ke yammacin sansanin ƴan gudun hijira na al Jadid a Nuseirat (a tsakiyar Zirin Gaza), inda suka kashe Falasɗinawa 36, galibinsu ƙananan yara da mata masu ciki," in ji sanarwar. Sojojin sun kai hari kan gidaje aƙalla 12 na fararen-hula a Gaza, a cewar sanarwar. Ta ƙara da cewa, "Muna ɗora alhakin ƙaruwar kisan ƙare-dangi da ake yi wa fararen-hula kan gwamnatin Amurka, da manyan ƙasashen duniya da Isra'ila the international. Su ne kanwa uwar gami na waɗannan laifukan yaƙi da ake aikatawa." Falasɗinawan da aka jikkata, ciki har da ƙananan yara a harin da aka kai sansanin ƴan gudun hijira na al-Maghazi da Deir al-Balah, an kai su Asibitin Al Aqsa da ke Gaza. / Hoto: AA