Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai a masallacin Jabalia na arewacin Gaza

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 0640 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a wu...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai a masallacin Jabalia na arewacin Gaza
Bu haberde ne var?

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 0640 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a wu...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 193 tana yi da Falasɗinawa da ke Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 33,797 da jikkata sama da mutum 76,465 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 0640 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai samame a wurare da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun kai samame a wurare da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan inda suka kashe Falasɗinawa da dama, a cewar ganau. Dakarun Isra'ila sun kai samame a birnin Qalqilya da ke arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, sannan sun kutsa kai cikin gidaje da dama a birnin, kamar yadda ganau suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu. Sun ƙara da cewa motocin sojojin Isra'ila sun riƙa buge motocin Falasɗinawa da gangan suna lalata su, yayin da kuma aka tura da sojojin Isra'ila gwanayen harbi daga ɓoye suka laɓe a rufin gidajen jama'a. Kazalika sojojin Isra'ila sun kai samame a garin Hableh da kudancin Qalqilya, inda suka kama aƙalla Falasɗinawa huɗu. Haka kuma an bayar da rahoton cewa dakarun Isra'ila sun kai samame a Tulkarem, Bethlehem, Ramallah, Hebron, da Jenin, inda suka tsare aƙalla Falasɗinawa biyar, a cewar ganau da suka gaya wa Anadolu. 0416 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a harin da ta kai ta sama a masallacin Jabalia na arewacin Gaza Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa da dama sannan suka jikkata wasu a harin da suka kai da sanyin safiya a masallacin Jabalia da ke arewacin Gaza, a cewar kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa WAFA. Majiyoyi daga asibiti sun ce “mutane da dama sun yi shahada sannan an kai mutum tara da suka jikkata Asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Zirin Gaza sakamakon harin da jiragen yaƙin masu mamaya suka kai Masallacin Al Fakhourada ke sansanin ƴan gudun hijira na Jabalia.” Kazalika motocin sojojin Isra'ila sun shiga garin Beit Hanoun da ke arewacin Gaza, inda suka mamaye wata makaranta da mutane suke samun mafaka tare da buɗe musu wuta, in ji WAFA. Majiyoyi a yankin sun ce an katse duk wata sadarwa ciki har da ta intanet a yankin Beit Hanoun a yayin da dakarun Isra'ila suka yi kutse. 0005 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa a Rafah Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu fararen-hula a yankin Tal al Sultan da ke Rafah, a yayin da ta kai sabon hari a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Gaza da kuma arewacin Gaza, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World. An kai wasu Falasɗinawa Asibitin Al Aqsa Martyrs sakamakon jikkatar da suka yi bayan harin da Isra'ila ta kai sansanin Nuseirat. / Hoto: AA 2200 GMT — Zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa ta ɓarke a wasu biranen Amurka Masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa sun toshe manyan hanyoyi a jihohin Illinois, California, New York da Oregon, lamarin da ya haddasa tarnaƙi ga masu zuwa Filin Jirgin Saman Ƙasa da Ƙasa na Chicago O'Hare, da gadojin Golden Gate and Brooklyn da ma hanyar West Coast mai cke da hada-hadar jama'a a yayin da Isra'ila ke ci gaba da mamaye Gaza. A Chicago, masu zanga-zanga sun toshe manyan hanyoyin da ke zuwa filayen jiragen sama da misalin ƙarfe bakwai na safe, a wani mataki da suka bayyana a matsayin "matsin lamba ta fuskar tattalin arziki domin ganin an bar Falasɗinawa sun sarara," a cewar Rifqa Falaneh, ɗaya daga cikin mutanen da suka jagorancin zanga-zangar. An katse tafiye-tafiye a birnin San Francisco na tsawon awanni a yayin da masu gangami suka toshe duk wasu manyan hanyoyin mota da na ƙafa da mahaya babura zuwa gadar Golden Gate Bridge inda suka kafa diram-diram cike da ƙasa da siminti suka toshe babbar hanyar Interstate 880 da ke Oakland. Masu zanga-zanga da suka yi tattaki a Brooklyn sun toshe hanyar da ke isa Manhattan daga kan Gadar Brooklyn. A yankin Eugene na Oregon, masu zanga-zanga sun toshe hanyar Interstate 5, inda suka kawo tsaiko a tafiye-tafiye na fiye da minti 45. An tura gomman ƴan sanda wurin da masu zanga-zanga suke yayin da suka toshe Gadar Golden Gate Bridge da ke San Francisco./Hoto:AA