Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0418 GMT — Isra'ila ta kas...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan
Em resumo

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0418 GMT — Isra'ila ta kas...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 327, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,476— galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,647, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Laraba, 28 ga watan Agusta 2024 0418 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare ta sama da samame da ta kai a wasu garuruwa da ke arewa da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, a cewar mai magana da yawun ƙungiyar bayar da agaji ta Red Crescent. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa biyu a birnin Jenin, da kuma mutum huɗu a wani ƙauye da ke maƙotaka da birnin, da mutum huɗu a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke kusa da garin Tubas, in ji Ahmed Jibril, jami'in ƙungiyar bayar da agajin.