Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 325, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,405 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,468, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024 0254 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Birnin Gaza City da Khan Younis Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama tare da jikkata wasu a harin da ta kai da bama-bamai a gidaje biyu a Birnin Gaza da Khan Younis na yankin Gaza da aka mamaye. "Mun karɓi gawawwakin shahidai da dama sakamakon luguden wuta da jiragen yaƙin Isra'ila suka yi a wani gida a Layin Al-Shuhada da ke Birnin Gaza," a cewar wani likita a Asibitin Baptist da ke Gaza a hira da Anadolu Agency . Ganau sun ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a gidan iyalan Abu Rida a garin Abasan al-Kabira da ke gabashin Khan Younis, inda suka kashe mutane da dama tare da jikkata wasu. 2104 GMT — Wakilan Hamas sun bar Alƙahira bayan nazari kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza Tawagar Hamas da ke cikin tattaunawar tsagaita wuta a Gaza ta bar birnin Alƙahira na Masar bayan ta yi nazari kan sakamakon tattaunawar baya bayan nan da Isra'la daga masu shiga tsakani na ƙasashen Masar da Qatar. Wani babban jam'i a Hamas Izzat al Rishq, ya wallafa saƙo a Telegram da ke cewa wakilansu "sun bar Masar da maraice bayan sun gana da masu shiga tsakani daga Masar da Qatar da kuma ji daga gare su game da sakamakon baya bayan nan kan tattaunawar tsagaita," ko da yake bai yi cikakken bayani ba. "Wakilanmu sun buƙaci masu mamaya su yi biyayya ga yarjejeniyar da aka amince da ita ranar 2 ga watan Yuli, kamar yadda yake a cikin shawarwarin Shugaban Amurka Joe Biden da Kwamitin Tsaro na MDD," in ji shi. Hamas ta jaddada aniyarta "ta aiwatar da jarjejeniyar da aka amince da ita domin cika muradun jama'armu da kuma dakatar da kai musu hari." Ya ƙara da cewa wakilansu sun "jaddada buƙatar ganin yarjejeniyar ta ƙunshi daina luguden wuta na dindindin, da janyewar Isra'ila daga Gaza da maido da mutane gidajensu da shigar da kayan agaji da sake gina yankin da kuma musayar waɗanda aka yi gakuwa da su." Wasu iyalai na Muammer suna jimamin kisan da Isra'ila ta yi wa ɗan'uwansu a Asibitin Shahidai na Al Aqsa a Deir Al Balah / Photo: AA 2216 GMT — Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta karɓi allurai fiye da miliyan 1 na cutar polio Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta sanar da cewa ta karɓi ruwan allura miliyan 1.26 domin yin rigakafin cutar shan inna. "A jimilla, allurai miliyan 1.26 na rigakafin OPV2 polio sun iso, tare da robobin ajiye su guda 500," in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar. "An soma shiri domin ƙaddamar da alluran rigakafin tare da abokan hulɗarmu," a cewar ma'aikatar, ba tare da yin ƙarin bayani ba.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama a Birnin Gaza City da Khan Younis
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 325, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,405 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,468, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024 0254 GMT — Isra'ila ta...

A taƙaice
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 325, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,405 — galibinsu mata da yara — tare da jikkata fiye da mutum 93,468, sannan an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024 0254 GMT — Isra'ila ta...
