Isra'ila ta kwashe kwana 278 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,243 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 88,033, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0625 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla takwas a wani hari ta sama da ta kai da daddare a wasu gidaje a tsakiyar Gaza a a yayin da ta shiga kwana na 278 tana luguden wuta a yankin, kamar yadda kafafen watsa labaran yankin suka ruwaito. Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa na Wafa ya ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa takwas, ciki har da yara shida, sannan ta jikkata mutane da dama a hare-hare ta sama da ta kai agidajensu a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat. Kazalika dakarun Isra'ila sun yi luguden wuta a yankuna daban-daban na Gaza, ciki har da harin da ta kai a gidajen da ke Titin Naser a arewacin Birnin Gaza da ya jikkata aƙalla mutum 10. I0111 GMT ––Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 29 a harin da ta kai a wata makaranta a Gaza; ta sa an rufe asibitoci Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 29 a harin da ta kai ta sama a wata makaranta da 'yan gudun hijira suke samun mafaka a kudancin Gaza ranar Talata, a yayin da luguden wutar da dakatunta suke ci gaba yi a arewaci ya sa aka rufe asibitocin Birnin Gaza tare da tilasta wa mutane tserewa daga gidajensu domin neman mafaka. Sojojin Isra'ila sun yi kisan kiyashi a makarantar Al-Awda da ke garin Abasan na gabashin Khan Younis, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar. Galibin yankunan Birnin Gaza sun kasance tamkar kufayi sakamakon luguden wutar da dakarun Isra'ila suka kwashe watanni tara suna yi a yankin. Yawancin mutanen da ke birnin sun tsere tun da aka fara yaƙin, amma dubban mutane na ci gaba da zama a arewaci. A watanni tara da Isra'ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, dakarunta sun mamaye asibitoci aƙalla takwas, inda suka kashe majinyata da ma'aikatan kiwon lafiya tare da lalata gine-gine da kayan aiki. Isra'ila ta yi zargin cewa ƙungiyar Hamas tana mafani da asibitocin ne domin ajiye makamai, ko da yake ba ta bayar da cikakkun shaidu game da zargin nata ba. Asibitoci 13 daga cikin 36 da ke Gaza ne suke aiki a halin yanzu, kuma su ɗin ba ba sa aiki kamar yadda ya kamata, a cewar ofishin jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya. An kai Falasɗinawa Asibitin Al-Aqsa Martyr domin yin jinya bayan Isra'ila ta kai musu hari a yankin Deir al-Balah / Hoto: AA 2239 GMT — Fadar White House ta zargi Iran da amfani da abin da ke faruwa a Amurka saboda rikicin Gaza don shisshigi cikin lamuran ƙasar, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, bayan wani gargaɗi da wani babban jami'in tattara bayanan sirri na Amurka ya yi cewa Iran na son rura wutar yanayin da ake ciki a Amurka. Gargaɗin, wanda Daraktan Hukumar Leƙen Asirin ƙasar Avril Haines ya yi, ya ce wasu mutane dake da alaƙa da gwamnatin Iran da suke bayyana kansu a matsayin farar-hula ne a shafukan sada zumunta, suna yunƙurin ƙarfafa gwiwar masu zanga-zanga, har suna ba su kuɗaɗe. Kakakin Fadar White House Karine Jean-Pierre ta ce 'yancin faɗin albarkacin baki na da muhimmanci ga dimokuraɗiyyar Amurka, sai dai gwamnati na da alhakin gargaɗin 'yan ƙasarta kan tasirin wasu daga ƙasashen waje. "Amurkawa daga kowane ɓangare da suke aiki da zuciya ɗaya, suna ƙoƙarin bayyana ra'ayinsu na ƙashin kansu kan rikicin Gaza. Idan aka yi amfani da 'yancin bayyana ra'ayoyi mabambanta cikin lumana hakan abu ne mai muhimmanci ga dimokraɗiyyarmu," kamar yadda ta bayyana, "A lokaci guda kuma, gwamnatin Amurka na da alhakin gargaɗin Amurkawa dangane da mummunan tasiri daga waje... Za mu ci gana da tona asirin duk wani yunƙuri na yi wa dimokuradiyyarmu ƙafar-ungulu kamar yadda muke yi a yau. An kai Falasɗinawan da aka jikkata ciki har da yara, Asibitn Shahidan na Al-Aqsa bayan harin Isra'ila a yankin Deir al-Balah . / Hoto: AA
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 8 cikinsu har da yara 6 a Gaza
Isra'ila ta kwashe kwana 278 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,243 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 88,033, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0625 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla takwas a wani hari ta sama da ta kai d...

لمحة سريعة
Isra'ila ta kwashe kwana 278 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,243 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 88,033, kana sama da mutum 10,000 na binne a ɓaraguzai. 0625 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla takwas a wani hari ta sama da ta kai d...
