الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 48 a Gaza a ƙasa da awa ɗaya

Isra'ila ta kwashe kwana 285 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,713 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,166, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0030 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare ta sama guda uku cikin ƙasa da awa ɗaya...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 48 a Gaza a ƙasa da awa ɗaya
لمحة سريعة

Isra'ila ta kwashe kwana 285 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,713 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,166, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0030 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare ta sama guda uku cikin ƙasa da awa ɗaya...

Isra'ila ta kwashe kwana 285 tana luguden wuta a Gaza inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 38,713 — galibinsu mata da yara –– sannan ta jikkata fiye da mutum 89,166, kana sama da mutum 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. 0030 GMT — Isra'ila ta kai hare-hare ta sama guda uku cikin ƙasa da awa ɗaya waɗanda suka kashe Falasɗinawa aƙalla 48 a Gaza, a cewar rundunar kare fararen-hula ta yankin. Isra'ila ta ce ta ta kai hare-hare biyu waɗanda rundunar kare fararen-hula ta ce sun jikkata mutanen da dama. Wasu sabbin alƙaluma da aka fitar sun nuna cewa mutum 25 sun mutu a makarantar Al Razi da ke cikin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat na tsakiyar Gaza wadda ke ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya, kamar yadda shugaban makarantar Mohammed al Mughair ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP. Kazalika dakarun Isra'ila sun kashe aƙalla mutum 18 sannan suka jikkata mutum 25 a harin da suka kai garin Al Mawasi da ke kusa da birnin Khan Younis na kudancin Gaza. Haka kuma sun kashe mutum biyar da ke tsaye a kusa da wani shatale-tale a garin Beit Lahia da ke Gaza, a cewar wasu jami'ai. 0140 GMT — Kafofin watsa labaran Lebanon sun ce yara uku na cikin mutum biyar da Isra'ila ta kashe a hare-hare ta sama Kafofin watsa labaran Lebanon sun ce hare-haren da dama da Isra'ila ta kai a kudancin ƙasar sun yi sanadin mutuwar mutum biyar cikinsu har da yara uku 'yan ƙasar Syria, yayin da ƙungiyar Hezbollah ta sanar da harba rokoki kan Isra'ila a matsayin martani. "Yara uku 'yan ƙasar Syria na cikin waɗanda maƙiya suka kashe" a harin da suka kai a wata gona a ƙauyen Umm Toot", a cear kamfanin dillancin abarai na National News Agency (NNA). Ya ƙara da cewa jirgi mara matuƙi na "maƙiya" ta kai hari kan 'yan Syria guda biyu da ke tafiya a kan baburi a hanyar Kfar Tebnit da ke kudancin Lebanon. Wata majiya a hukumar tsaron Lebanon wadda ba ta so a ambaci sunanta, ta shaida wa kamfanin dillancin labara na AFP cewar 'yan Syrian biyu da aka kashe "fararen-hula" da ke aiki a kusa da inda aka kai harin.