Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,204 da jikkata fiye da 101,640, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. Juma'a, 1 ga watan Nuwamba, 2024 2346 GMT — Falasɗinawa aƙalla 26 ne suka mutu kana 47 suka jikkata sakamakon hare-hare ta sama da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai a faɗin yankin Gaza, a cewar wasu majiyoyi na asibiti. Da farko, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a wani gida da ke yankin Sabra a kudancin Birnin Gaza, inda suka kashe Falasɗinawa biyu da jikkata huɗu, in ji majiyoyin. Kazalika, wani hari da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai kan wani taron jama'a a garin Al-Zawayda da ke yankin tsakiyar Gaza ya kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata mutum uku. Bugu da ƙari, wasu hare-hare da sojojin Isra'ila suka kai a gidaje biyu da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke arewacin Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 16 da jikkata 30, ciki har da ƙananan yara. Majiyoyin sun ƙara da cewa Falasɗinawa huɗu sun mutu sannan goma sun jikkata, ciki har da yara, a wani luguden wuta da dakarun Isra'ila suka yi a gidansu da ke arewa maso yammacin Birnin Gaza. Sai kuma Falasɗinawa biyu 'yan'uwan juna da jiragen yaƙin Israila suka kashe tare da jikkata gomman lokacin da suka kai harin bam a wani gida da ke Deir al-Balah a tsakiyar Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka shaida wa kamfani dillancin labarai na Anadolu Agency . Ƙarin labarai ???? 0349 GMT — Rokokin da aka harba daga Lebanon sun kashe mutum 7 a Isra'ila ciki har da 'yan ƙasar Thailand huɗu Rokokin da aka harba daga Lebanon zuwa arewacin Isra'ila sun kashe ma'aikata 'yan ƙasashen waje huɗu da 'yan Isra'ila uku, a cewar ma'aikatan asibitin Isra'ila, wanda shi ne hari mafi muni da aka kai wa Isra'ila tun da ta soma mamayar Lebanon. Thailand ta tabbatar da cewa 'yan ƙasar huɗu na cikin waɗanda suka mutu sakamakon harin na rokoki. Ministan Harkokin Wajen Thailand, Maris Sangiampongsa ya wallafa saƙo a shafinsa na X inda ya bayyana "matuƙar baƙin ciki" bisa kisan da aka yi wa 'yan ƙasarsa a kusa da garin Metula ranar Alhamis, inda ya ƙara da cewa an jikkata wani ɗan ƙasar tasu guda ɗaya.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 26 a sabbin hare-hare da ta kai a faɗin Gaza
Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,204 da jikkata fiye da 101,640, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. Juma'a, 1 ga watan Nuwamba, 2024 2346 GMT — Falasɗin...

At a glance
Yaƙin kisan ƙare-dangi na Isra'ila a Gaza - da ke cikin kwanaki 392 - ya kashe kusan mutum 43,204 da jikkata fiye da 101,640, kuma ana fargabar mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 2,865 tun daga Oktoban bara. Juma'a, 1 ga watan Nuwamba, 2024 2346 GMT — Falasɗin...
