الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 10 a faɗin Gaza

Yaƙin Isra'ila a Gaza, wanda ya shiga kwana na 295, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,175 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata sama da mutum 90,403, kuma an yi amanna mutum fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024 2101 GMT — Isra'i...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 10 a faɗin Gaza
لمحة سريعة

Yaƙin Isra'ila a Gaza, wanda ya shiga kwana na 295, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,175 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata sama da mutum 90,403, kuma an yi amanna mutum fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024 2101 GMT — Isra'i...

Yaƙin Isra'ila a Gaza, wanda ya shiga kwana na 295, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,175 — galibinsu mata da yara –– sannan ya jikkata sama da mutum 90,403, kuma an yi amanna mutum fiye da 10,000 na binne a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. Asabar, 27 ga watan Yuli, 2024 2101 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a hare-hare da ta kai ta sama a faɗin Gaza, in ji rundunar da ke kare fararen-hula ta yankin. A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce an kashe Falasɗinawa shida tare da jikkata gommai a hari ta sama da Isra'ila ta kai a gidaje biyu, a garin Zawayda da ke tsakiyar Gaza da kuma kuma birnin Khan Younis da ke kudanci. Kazalika a wata sanarwa ta daban, rundunar da ke kare fararen-hula ta Falasɗinu ta ce Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu a wani hari ta sama da ta kai kan wani taron mutane a yankin Al-Kateeba da ke Khan Younis. Haka kuma a sanarwa ta uku, rundunar ta ce dakarun Isra'ila sun kai samame a kan wani taron jama'a a yammacin Birnin Gaza inda suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu. Sannan mutane da dama sun jikkata sakamakon luguden wuta da sojojin Isra'ila suka yi a wani gida a yammacin sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke tsakiyar Gaza, a cewar rundunar da ke kare fararen-hula ta yankin. 2323 GMT — Amurka ta yi iƙirarin lalata jirage 6 marasa matuƙa na Houthi, jiragen ruwa 3 a Yemen Rundunar sojin Amurka ta yi iƙirarin lalata jirage shida marasa matuƙa na Houthi a yankin da ƙungiyar ta mamaye da kuma jiragen ruwa uku da ke aiki a gaɓar tekun Yemen, kamar yadda Rundunar Bayar da Amurka ta Amurka (CENTCOM) ta bayyana. "An yi amannar cewa waɗannan makamai suna barazana ga Amurka da dakarun da kuma jiragen ruwa na 'yan kasuwa," a cewar saƙon da CENTCOM ta wallafa a shafin X. "An ɗauki matakin ne domin kare 'yancin walwala a cikin teku tare da tabbatar da tsaron teku ga masu jigila a cikinsa daga ƙasashen duniya," in ji sakon.