Início / Arquivo de notícias
Arquivo de notícias

Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya

Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin J...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Atualizado 13/08/2026, 05:26:13
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya
Em resumo

Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin J...

Tsawon kwanaki 101, Isra'ila tana ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza a yayin da Firaiminista Netanyahu ya lashi takobin ci gaba kai wadannan hare-hare wadanda suka jawo asarar rayuka 23,968 da raunata mutum 60,582. 0858 GMT — Isra'ila ta kashe karin Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu ta bayyana cewa Isra’ila ta kashe Falasdinawa biyar a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce akwai wani yaro dan shekara 14 wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon wutar da Isra’ila ta bude a sansanin ‘yan gudun hijira na birnin Jericho. Kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar WAFA ya bayyana, dakarun na Isra’ila sun harbi yaron a kirji a yayin da suka kai hari sansanin. 0828 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 60 a cikin dare daya Isra'ila ta kashe sama da Falasdinawa 60 a a cikin dare guda a Gaza a sakamakon hare-haren da take ci gaba da kaiwa, kamar yadda Ma'aikatar Lafiya ta Falasdinu ta tabbatar. Ma'aikatar ta bayyana cewa akwai gomman mutane wadanda aka raunata a sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa na atilare a cikin Gaza. Hare-haren sun fada a cikin biranen Khan Younis da Rafah duka wadanda suke kudanci, da kuma wasu wurare da ke cikin Zirin Gaza, kamar yadda ofishin watsa labaran ya tabbatar.