Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 110 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza —Kungiyoyar Fursunonin Falasdinu Wata kungiya mai zaman kanta ta Falasdinu ta zargi sojojin Isra'ila da kashe Falasdinawa 30 a Gaza. "An gano gawarwakin mutum 30 da aka daure wa hannu da kuma rufe musu idanu a cikin wata makaranta a Beit Lahia da ke arewacin Gaza," in ji kungiyar fursunonin Falasdinu a cikin wata sanarwa a ranar Laraba. Ya ce Falasdinawan da suka mutu sojojin Isra'ila ne suka tsare su kafin mutuwarsu. "A bayyane yake cewa sojojin mamaya sun aiwatar da hukuncin kisa a kan wadannan mutane," in ji kungiyar. Kungiyar ta ce hukumomin Isra'ila sun ƙi bayar da bayanai game da makomar Falasdinawa da sojojin Isra'ila ke rike da su a Gaza. 1202 GMT — Sojojin Isra'ila sun janye wata rundunar dakarunsu ta ko-ta-kwana daga Gaza Sojojin Isra'ila sun janye sojojin kiyaye zaman lafiya na runduna ta 5 daga Gaza, kamar yadda kafafen yada labaran Isra'ila suka bayyana. Kamfanin dillancin labaran Isra'ila KAN ya rawaito cewa dakarun ko-ta-kwana na runduna ta 5 sun yi yaƙi a Arewacin Gaza tare da ƙwace yankin gabar tekun wajen daga hannun mayakan Hamas. A cewar kafar yada labaran, wata rundunar ko-ta-kwana daya ce kawai ta rage a yankin Falasdinu. Har yanzu dai ba a san adadin sojojin Isra'ila da aka jibge a Gaza ba. 0944 GMT — Adadin Falasdinawa da suka mutu ya kai 26,900 a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce akalla mutum 26,900 ne aka kashe a yankin Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya tun bayan barkewar yakin da Isra'ila ke yi a ranar 7 ga watan Oktoba. Rahoton na baya-bayan nan ya hada da mutuwar mutum 150 a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji sanarwar ma'aikatar, ta kuma kara da cewa mutum 65,949 ne suka jikkata a Gaza tun bayan barkewar fadan. 0903 GMT — Isra'ila ta ƙara rasa sojojinta uku a Gaza Rundunar Sojin Isra’ila ta sanar da cewa ta rasa ƙarin sojojinta uku a yaƙin da take yi da Falasɗinawa a Zirin Gaza, kamar yadda rundunar sojin ƙasar ta sanar a ranar Laraba. A wata sanarwa daga shafin jaridar Times of Israel, rundunar sojin ta Isra’ila ta ce akwai sojojinta biyu waɗanda aka ji wa mummunan rauni a kudancin Gaza. Adadin sojojin Isra’ila da aka kashe tun bayan soma wannan yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 560. 0830 GMT — Isra'ila ta umarci Falasɗinawa 88,000 su fice daga yammacin Gaza Isra'ila ta ƙara bayar da wani sabon umarni ga Falasɗinawa akalla 88,000 waɗanda suka rasa muhallansu da ke zaune a yammacin birnin Gaza kan su tashi daga wurin, kamar yadda Hukumar Kula da Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar. Yankin wanda ya haɗa da sansanin ƴan gudun hijira na Ash Shati, ya kasance wuri da ke da mazauna kusan 300,000 kafin fara yakin. Tun bayan fara wannan yaƙin a ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila ta bai wa mazauna Gaza wa'adi kan su fice daga birnin.
Taskar labarai
Wannan sashe yana nuna tsoffin labarai da ranakun da aka wallafa su. An nuna labarin a harshensa na asali.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe Falasdinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza — Kungiyar Fursunonin Falasdinu
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 110 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza —Kungiyo...

A taƙaice
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 117 tana kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 26,751 sannan suka jikkata mutum 65,636, a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta babu kakkautawa a yankin. 110 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 30 da ke tsare a hannunta a Gaza —Kungiyo...
