Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 144 - ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 29,782, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 69,879. 0212 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Yammacin Gabar Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ruruwa Kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na WAFA ya rawaito cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku a yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan da suka mamaye. An kashe mutanen ne a harin da aka kai a garin Tubas da kuma sansanin Al-Far’a da ke kusa da Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, in ji sanarwar. Aƙalla Falasdinawa 400 ne sojojin Isra'ila da wasu Yahudawa 'yan kaka gida suka kashe tun ranar 7 ga watan Oktoba. 2300 GMT — Biden ya ce tsagaita wuta na Gaza na gab da yiwuwa yayin da Isra'ila ke shirin mamaye Rafah Shugaban Amurka Joe Biden ya ce yana fatan tsagaita wuta a Gaza da aka yi wa ƙawanya ka iya fara aiki a farkon mako mai zuwa. Da ya ziyarci birnin New York, an tambayi Biden lokacin da tsagaita wuta a yankin Falasdinawa da aka killace zai iya farawa, ya kuma amsa da cewa, "Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa ya gaya mini cewa muna kusa, mun kusa, ba mu gama ba tukuna. Fatana shi ne nan da Litinin mai zuwa za a tsagaita wuta."
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Yammacin Gabar Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ruruwa
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 144 - ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 29,782, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 69,879. 0212 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Yammacin Gabar Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ruruwa Kamfanin dillan...

At a glance
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza - wanda yanzu ya shiga kwana na 144 - ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa aƙalla 29,782, galibi yara da mata, tare da jikkata wasu 69,879. 0212 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 3 a Yammacin Gabar Kogin Jordan yayin da yaƙin Gaza ke ci gaba da ruruwa Kamfanin dillan...
