الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 194 tana kai wa Falasɗinawa da ke Gaza sun kashe aƙalla mutum 33,843 da jikkata sama da mutum 76,575 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 2100 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza
لمحة سريعة

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 194 tana kai wa Falasɗinawa da ke Gaza sun kashe aƙalla mutum 33,843 da jikkata sama da mutum 76,575 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 2100 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 194 tana kai wa Falasɗinawa da ke Gaza sun kashe aƙalla mutum 33,843 da jikkata sama da mutum 76,575 a yayin da ƴan-kama-wuri-zauna da dakarun Isra'ila wajen kashe Falasɗinawa da ke Yammacin Kogin Jordan. 2100 GMT —Isra'ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 28, cikinsu har da ƙananan yara da dama, a sabbin hare-hare da ta kai wurare dban-daban a yankin Gaza da ta mamaye, kamar yadda ganau suka shaida wa TRT World da kafafen watsa labaran yankin. Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe mutum takwas a yankin Tuffah bayan sun kai hari kan wata motar ƴan sanda. Kazalika luguden wutar da Isra'ila ta yi a sansanin al-Maghazi da ke yankin Deir al-Balah na Gaza ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 13. Haka kuma Isra'ila ta kashe Falasɗinawa bakwai a harin da ta kai wa wasu iyalai a sansanin Yabna da ke birnin Rafah. Ta jikkata mutane da dama a harin.