Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 2030 GMT — Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa aƙalla12 tare da jikkata gommai a hare-haren da ta kai a yankuna da dama na Gaza. An kashe mutum uku ne lokacin da jirgi mara matuƙi ya kai hari a kan babur ɗinsu a arewacin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda ma'aikatan kiwon lafiya suka shaida wa Anadolu Agency. Kazalika wasu majiyoyi sun ce an kashe Falasɗinawa huɗu a harin da Isra'ila ta kai ofishin 'yan sanda na Asdaa da ke Khan Younis. Bugu da ƙari an kashe Falasɗinawa biyu tare da jikkata wasu da dama a a harin da dakarun Isra'ila suka kai kan wani rukuni na jama'a a yankin Abasan Al-Kabira da ke gabashin Khan Younis. Wata sanarwa da asibitin Al Awda ya fitar ta ce an kai hari ta sama a gidan iyalan Abu Jarboa da ke sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat inda Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyu. A Birnin Gaza, Isra'ila ta kashe wani Bafalasɗine, tare da jikkata gommai a wani hari ta sama da ta kai a taron jama'a a unguwar Shujaiyya da ke gabashin birnin.
Haber arşivi
Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa aƙalla 12 a Gaza
Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 2030 GMT — Isra'ila ta k...

Bu haberde ne var?
Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda yau ya shiga kwana na 458 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,805 tare da jikkata fiye da mutum 109,064. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,048 tun daga watan Okotban 2023 Litinin, 6 ga watan Janairu, 2025 2030 GMT — Isra'ila ta k...
