Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki har da jarirai 10 a Gaza

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0830 —Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki har da jarirai 10 a Gaza
Bu haberde ne var?

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0830 —Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki...

Isra'ila ta kwashe kwana 230 tana kai hare-hare a Gaza abin da ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 35,709 — galibinsu jarirai da mata da yara — sannan ta jikkata sama da mutum 79,990, kuma mutum sama da 10,000 na binne a ɓaraguzan gine-gine. 0830 —Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 25, ciki har da jarirai 10 a Gaza Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla 17, waɗanda suka haɗa da fiye da ƙananan yara 10, sannan suka jikkata gommai a hare-haren da suka kai gidaje biyu a Birnin Gaza da Rafah. A sansanin 'yan gudun hijira na Al-Nuseirat, sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla takwas. Wasu ganau sun ce jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa 16, ciki har da yara 10, kana suka jikkata mutane da dama a harin da suka kai wani gida a yankin Al-Daraj na Birnin Gaza. Kazalika, wasu majiyoyi sun ce dakarun Isra'ila sun kashe wani Bafalasɗine yayin da suka kai hari a gidan wani mutum mai suna Al-Sha'er a Rafah da ke kudancin Gaza. 0125 GMT — Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a kusa da ofishin Netanyahu Ɗaruruwan Isra'ilawa sun yi zanga-zanga a ƙofar ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu lokacin taron majalisar ministoci ta yaƙi, suna neman a sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza. Zanga-zanga ta kuma ɓarke a biranen Isra'ila da dama bayan an wallafa wani bidiyo da ke nuna mayaƙan Hamas sun kama wata sojan Isra'ila a wani sansanin sojoji da ke matsugunin Yahudawa na Nahl OZ a kusa da katangar Gaza a ranar 7 ga Oktoban bara. A cikin wata sanarwa, Hamas ta ce "an jirkita bidiyon wanda ake yaɗawa a kafofin watsa labaran Isra'ila sannan ba ma za a iya tabbatar da sahihancinsa ba." Ta ƙara da cewa "yaɗa bidiyon na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta gaza ɓata sunanmu ta hanyar yaɗa labaran da aka ƙirƙira da aka tabbatar da cewa na ƙarya ne, ta hanyar kafofin watsa labarai da dama da kuma bincikin da kafofin watsa labarai suka dinga yi." Wata jaridar Isara'ila Haaretz ta rawaito cewa mambobin majalisar yaƙin Benny Gantz da Gadi Eizenk da Ministan Tsaro Yoav Gallant sun gana da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su kafin a fara taron, amma Netanyahu bai ba da amsa ba ga buƙatar mutanen ta ganawa da shi. Isra'ilawa sun buaci Firaminista Benjamin Netanyahu ya sauka daga muƙaminsa sanna ya gudanar da sabon zaɓe. / Photo: AFP