Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 382, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,603 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,483 a Lebanon tun Oktoban bara. 0654 GMT — Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da sojojin Isra'ila suka kai a arewacin Gaza, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa Anadolu. A cewar wata majiyar lafiya, Falasdinawa 12 ne suka mutu yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon luguden wuta da Isra'ila ta yi kan 'yan gudun hijira a Beit Lahia. Shaidu sun ce jirage marasa matuka sun kewaye makarantar Khalifa Bin Zayed, inda jami'ai suka yi barazanar kashe su idan ba su tashi ba. Wata majiyar likitocin ta ce an kashe wasu Falasdinawa takwas a harin da Isra'ila ta harba makaman atilari a yankin Al Alami da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia. 0555 GMT — Sojojin Isra'ila sun kori daruruwan Falasdinawa daga matsugunai a garin Beit Lahia da ke arewacin Gaza, tare da yi musu barazana da makamai. A cewar rahotanni daga fararen hular da suka rasa matsugunnansu, sojojin Isra'ila da suka shafe akalla kwanaki 17 suna kai hare-hare tare da killace arewacin Gaza, sun kai samame a wata mafaka da ke kusa da asibitin Indonesiya inda Falasdinawa suka fake. Sojojin sun tsare wani adadi mai yawa na Falasdinawa maza da ke zama a wurin.
Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 20 a arewacin Gaza
Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 382, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,603 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,483 a Lebanon tun Oktoban bara. 0654 GMT — Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe a w...

Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 382, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,603 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,483 a Lebanon tun Oktoban bara. 0654 GMT — Akalla Falasdinawa 20 ne aka kashe a w...
