Inicio / Archivo de noticias
Archivo de noticias

Esta sección muestra noticias archivadas con sus fechas de publicación originales. El artículo se muestra en su idioma original.

Kai-tsaye: Isra’ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 11 a ci gaba da kisan ƙare-dangi a Gaza

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 407 — ya kashe aƙalla Falasɗinawa 43,764 da jikkata 103,480, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,440 tun Oktoban bara. 2049 GMT — Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 11 ta jik...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Actualizado 13/8/2026, 5:26:13
Kai-tsaye: Isra’ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 11 a ci gaba da kisan ƙare-dangi a Gaza
De un vistazo

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 407 — ya kashe aƙalla Falasɗinawa 43,764 da jikkata 103,480, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,440 tun Oktoban bara. 2049 GMT — Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 11 ta jik...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza — wanda a yanzu ya shiga kwana na 407 — ya kashe aƙalla Falasɗinawa 43,764 da jikkata 103,480, kuma ana fargabar 10,000 suna binne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon ma, Isra'ila ta kashe mutum 3,440 tun Oktoban bara. 2049 GMT — Isra’ila ta kashe Falasɗinawa 11 ta jikkata wasu da dama a ruwan bama-bamai da ta yi kudanci da arewacin Gaza, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na WAFA. Kamfanin dillancin labaran na Falasɗinawa ya ce masu mamaya na Isra’ila sun kashe fararen hula huɗu sun kuma jikkata da dama a hare-haren da suka kai unguwar al-Karama a arewacin Birnin Gaza. Sojojin na Isra’ila sun kuma kashe wasu mutanen biyu sannan sun jikkata wasu bayan sun jefa bam wani gida a unguwar Zeitoun dake kudu maso gabshin birnin. Kamfanin dillancin labaran ya ƙara da cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani matashi lokacin da yake yunƙurin guduwa daga arewacin Gaza zuwa tsakiyar birnin, don kauce wa yankin da aka killace. A kudancin Gaza kuwa, masu aikin ceto sun ton gawawwakin wasu fararen hula huɗu da aka kashe a hare-haren Isra’ila ta sama a wurare daban-daban a Rafah.