Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 1135 GMT –– Isra'ila ta kashe ƙananan yara 8 a sabbin hare-haren da ta kai Gaza Isra'ila ta kashe Falasɗinawa sama da goma sha biyu, ciki har da ƙananan yara takwas a harin bam da ta kai Gaza ranar Asabar, a cewar kafar watsa labaran Falasɗinu. Ta kai harin ne a wani gida da ke yankin Saudi na birnin Rafah. Falasɗinawa aƙalla shida, ciki har da ƙananan yara huɗu ne suka mutu a wannan harin, in ji kamfanin labarai na Wafa. Kazalika mutum aƙalla takwas sun jikkata. Haka kuma jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankin Jaradat da ke gabashin Rafah, inda suka jikkata mutane da dama, kamar yadda ganau suka tabbatar wa da kamfanin labarai na Anadolu. A Gaza, harin da Isra'ila ta kai ta sama a sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa tara, cikinsu har da ƙananan yara huɗu, tare da jikkata mutum 30, a cewar majiyoyi daga asibitin yankin. Wani wakilin Anadolu ya ce ma'aikatan ceto sun zaƙulo gawawwaki huɗu da kuma mutane da dama da suka jikkata a ƙarƙashin ɓaraguzan wani gini awanni bayan Isra'ila ta kai masa hari ta sama. Sannan jiragen yaƙin Isra'ila sun yi ɓarin wuta a sansanonin Nuseirat da Bureij kana suka rusa wasu gidaje a garin Al-Mughraqa na tsakiyar Gaza, in ji shi. 0914 GMT — Adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a Gaza ya kai 34,388 Ma'aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu ta ce kawo yanzu adadin mutanen da Isra'ila ta kashe a yankin ya kai 34,388. Mutanen da suka mutu sun haɗa da mutum 32 da dakarun Isra'ila suka kashe a awanni 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar kiwon lafiyar. Ta ƙara da cewa mutane 77,437 sun jikkata a Gaza tun da Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a yankin ranar 7 ga watan Oktoba. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla 32 tare da jikkata 69 a hare-haren da ta kai Gaza a cikin awa 24 da suka gabata, a cewar ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu./Hoto: OTHER 0906 GMT — Mutum ɗaya ya mutu yayin da Isra'ila ta yi luguden wuta a wasu garuruwa na kudancin Lebanon Aƙalla mutum guda ya mutu a Lebanon yayin da jiragen yaƙin Isra'ila suka kai hare-hare biyu a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa da ke kudancin ƙasar. "Jiragen yaƙin Isra'ila sun kai samame sau biyu da sanyin safiya a garuruwan Kafr Shuba da Shebaa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar Qasim Asaad a garin Kafr Shuba da kuma rusa gidaje biyus," a cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon. Kawo yanzu Isra'ila ba ta ce komai game da wannan batu ba. 0043 GMT — Hamas ta ce tana nazari kan sabbin sharuɗɗan tsagaita wuta na Isrra'ila Ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta karbi bayanai daga Isra'ila game da sabbin sharuddan tsagaita wuta a Gaza da kuma sakin mutanen da aka yi garkuwa da su kuma tana yin nazari a kansu. "A yau, ƙungiyar Hamas ta karɓi bayabai daga Yahudawa ƴan mamaya game da batun tsagaita, waɗanda masu shiga tsakanin daga Masar da Qatar suka gabatarranar 13 ga watan Afrilu," a cewar Khalil al Hayya, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas, a wata taƙaitacciyar sanarwa da ya fitar. "Ƙungiyarmu za ta yi nazari a kansu, kuma da zarar mun kammala za mu bayar da amsa." Khalil al Hayya, mataimakin shugaban ɓangaren siyasa na Hamas ya ce za su fitar da matsayarsu da zarar sun gama nazari kan bayanai da Isra'ila ta miƙa musu./Hoto: AFP
Arquivo de notícias
Esta secção apresenta notícias arquivadas com as datas de publicação originais. O artigo é apresentado no idioma original.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe ƙananan yara 8 a sabbin hare-haren da ta kai Gaza
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 1135 GMT –– Isra'ila ta kashe ƙananan yara 8 a sa...

Em resumo
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe kwana 204 tana yi a Gaza ya kashe 34,388 Falasɗinawa — kashi 70 daga cikinsu jarirai da ƙananan yara da mata — sannan mutum sama da 77,437 sun jikkata, yayin da ake fargabar mutum 8,400 na ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine. 1135 GMT –– Isra'ila ta kashe ƙananan yara 8 a sa...
