الرئيسية / أرشيف الأخبار
أرشيف الأخبار

يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 30 a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 434 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,835 tare da jikkata mutum fiye da 106,356. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. 2100 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 30 tare da jikkata 40 a...

NewstimeTR Haber Merkezi · · آخر تحديث 13‏/8‏/2026، 5:26:13 ص
Kai-tsaye: Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 30 a sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da ke Gaza
لمحة سريعة

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 434 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,835 tare da jikkata mutum fiye da 106,356. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. 2100 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 30 tare da jikkata 40 a...

Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana 434 — ya kashe Falasɗinawa aƙalla 44,835 tare da jikkata mutum fiye da 106,356. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum fiye da 4,047 tun daga Oktoban 2023. 2100 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 30 tare da jikkata 40 a harin da ta kai ta sama a wani gida da ke sansanin Nuseirat da ke Gaza da aka yi wa kawanya. Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan gidaje da gine-gine da dama a sansanin, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya ruwaito. Rahotanni sun nuna cewa akasarin wadanda aka kashe da kuma jikkata mata ne da kananan yara. Shaidu sun bayar da rahoton barna sosai a yankin, inda motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaro suka ci gaba da neman mutanen da suka bace a karkashin baraguzan ginin. 2048 GMT — Dakarun Isra'ila sun tare ayarin motocin Majalisar Dinkin Duniya dauke da man fetur da kayayyakin kiwon lafiya da nufin tallafawa asibitin Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, in ji darektan asibitin. A cikin wata sanarwa ta bidiyo, Hussam Abu Safiya ya ce tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da mu cewa, sojojin Isra'ila sun hana ayarin motocin da ke dauke da man fetur da magunguna masu muhimmanci shiga, lamarin da ya tilasta musu komawa kudancin Gaza. Da yake karin haske kan halin da ake ciki, ya ce: "Akwai matukar karancin kayayyakin jinya da ake bukata don jinyar wadanda suka jikkata da ke isa asibiti. Muna gudanar da ayyuka kaɗan-kaɗan saboda ƙarancin kayan aiki."