Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 219, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,971 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,641 ne suka jikkata. 0503 GMT — Isra’ila ta kai sabon hari Gaza, likitoci biyu sun rasu Isra’ila ta sake ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Gaza bayan ta faɗaɗa hare-haren da take kaiwa zuwa Rafah, inda Majalisar Ɗinkin Duniya ke ci gaba da gargaɗi kan cewa kai hari a Rafah da ke cike da mutane zai iya kasancewa babban bala’i. Hukumar tsaro ta farin kaya ta Gaza ta ce an kashe likitoci biyu a ranar Lahadi a garin Deir al Balah, inda kafafen watsa labarai suka ruwaito cewa an samu arangama mai muni da luguden wuta ta sama da ƙasa a kusa da Gaza. Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa Isra’ila ta kai hari a kusa da mashigar Rafah a ranar Asabar, inda hotuna suka nuna yadda hayaƙi ya rinƙa tashi 2258 GMT — Faransa ta yi Allah wadai kan harin Isra’ila a Rafah Faransa ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai Rafah, kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta bayyama. “Babu wani wuri mai aminci ga farar hula a Gaza,” kamar yadda ta bayyana, inda ta yi kira ga Isra’ila ta dakatar da kai hare-hare. Sanarwar ta buƙaci Isra’ila ta koma tattaunawa da Gaza sakamakon “ita ce hanya ɗaya kacal da za a sako waɗanda ake tsare da su da kuma samun dawamammiyar tsagaita wuta.” 2252 GMT — Ɗaliban Yemen sun yi tattaki domin nuna goyon baya ga Gaza Ɗaliban jami’o’i sun gudanar da zanga-zanga a arewacin Yemen domin nuna goyon bayansu ga Gaza, wadda ke ci gaba da shan baƙar wuya a hannun Isra’ila sakamakon hare-haren da take kai mata. Ɗaruruwan mutane ne suka taru a arewacin lardin Al-Jawf domin nuna goyon baya ga Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai mata hari, kamar yadda gidan talabijin na Al-Masirah da ke ƙarƙashin jagorancin Houthi ya nuna. A yayin da suke ɗauke da tutocin Falasɗinu, masu zanga-zangar sun nuna rashin jin daɗinsu dangane da zaluncin da Isra’ila ke aikatawa. Sun ta faɗin kalamai na ƙin jinin Isra’ila inda suke nuna goyon bayansu ga jama’ar Gaza.
News archive
This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.
Kai-tsaye: Isra’ila ta kai sabon hari Gaza, likitoci biyu sun rasu
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 219, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,971 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,641 ne suka jikkata. 0503 GMT — Isra’ila ta kai sabon hari Gaza, likitoci biyu sun rasu Isra’ila ta sake ƙaddamar...

At a glance
Yaƙin Isra'ila a Gaza ya shiga kawana na 219, inda ya yi sanadin mutuwar aƙalla Falasɗinawa 34,971 — waɗanda kashi 70 daga cikinsu jarirai ne da yara da mata — sannan sama da mutum 78,641 ne suka jikkata. 0503 GMT — Isra’ila ta kai sabon hari Gaza, likitoci biyu sun rasu Isra’ila ta sake ƙaddamar...
