Yaƙin da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,870. Kazalika, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon tun Oktoban 2023 inda ta kashe fiye da mutum 2,000, ta raba fiye da mutum miliyan 1.2 da muhallansu. 2014 GMT — Kafofin watsa labaran gwamnatin Lebanon sun bayar da rahotannin da ke cewa Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a kudancin Beirut jim kaɗan bayan wa'adin da sojojin Isra'ila suka bai wa mazauna yankunan domin barin wuraren ya cika — inda suke ta yin luguden wuta. "Jiragen yaƙin abokan gaba sun ƙaddamar da hare-hare biyu a yankunan da ke bayan garin kudancin Beirut, da farko sun kai hari a yankin Saint Therese, daga bisani suka kai hari a yankin Burj al-Barajneh," a cewar kamfanin dillancin labaran Lebanon National News Agency . 0307 GMT — An kashe sojin Isra'ila ɗaya a ba-ta-kashi a arewacin Isra'ila, in ji rundunar sojin ƙasar Rundunar sojojin Isra'ila ta fitar da sanarwa da sanyin safiyar Litinin da ke cewa an kashe sojanta ɗaya yayin ba-ta-kashi a kan iyakar Lebanon sannan an jikkata sojoji biyu. 2036 GMT — An ɗage dakatarwar da aka yi ta tashin jiragen sama a Iran An ɗage matakin da hukumomin Iran suka ɗauka na dakatar da tashin jiragen sama domin tabbatar da tsaron lafiyarsu, a cewar kafofin watsa labaran gwamnati, kamar yadda hukumar kula da sufurin jiragen sama ta sanar tun da farko. 1923 GMT — Hezbollah ta ce ta kai hari kan wani taron sojojin Isra'ila a yankunan da ke arewa Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon ta ci gaba da yin luguden wuta a yankunan sojoji da kuma wani taro na sojojin Isra'ila a matsugunan da ke arewaci inda ta yi amfani da jirage mara matuƙa da rkoki wajen kai hare-haren. A wasu saƙonni da ta wallafa a shafin Telegram, ƙungiyar ta ce mayaƙanta sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da jirage marasa matuƙa a bataliyar soji mai lamba 7200 da kuma sansanin sojoji da ke kudancin Haifa, inda ta samu "wuraren da aka nufa kai-tsaye". Kazalika Hezbollah ta ce mayaƙanta sun yi luguden wuta a kan wani taro sojojin Isra'ila a matsugunin Ma'alot Tarshiha "da rokoki da dama".
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a kudancin Beirut
Yaƙin da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,870. Kazalika, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon tun Oktoban 2023 inda ta kashe fiye da mutum 2,000, ta raba fiye da mutum miliyan 1.2 da muhallansu. 2014 GMT — Kafofin watsa labaran gwamnatin Lebanon...

Yaƙin da Isra'ila ta kwashe shekara guda tana yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 41,870. Kazalika, Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Lebanon tun Oktoban 2023 inda ta kashe fiye da mutum 2,000, ta raba fiye da mutum miliyan 1.2 da muhallansu. 2014 GMT — Kafofin watsa labaran gwamnatin Lebanon...
