Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasɗinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0700 GMT — Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama a sansanin Nuseirat da Rafah Falasɗinawa aƙalla uku sun mutu sannan wani mutum ɗaya ya jikkata sakamakon wani hari ta sama da dakarun Isra'ila suka kai tsakiyar Gaza. Wata majiyar asibitin ta shaida wa Anadolu Agency cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari ne a kan wani rukunin mutanea makarantar Al Arban da ke sansanin ƴan gudun hijira na Nuseirat, inda mutanen uku suka mutu. An kai gawawwakin mutanen asibitin Al Awda da ke cikin sansanin. Kazalika jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a arewa maso yammacin sansanin ƴan gudun hijirar, a cewar kamfanin dillancin Falasɗinawa na Wafa. Ranar Laraba, majiyoyi daga asibiti da jami'an tsaro a Gaza sun bayar da rahotannin da ke cewa jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a Rafah da kuma sansanin Nuseirat. Bugu-da-ƙari, jiragen yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankuna da dama da ke Gaza. 0200 GMT — Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra'ila Majalisar Dattawan Amurka ta amince a bai wa Isra’ila tallafin soji har na dala biliyan 26.6, ga ƙawar tata da ake zargi da yi wa Falasɗinawan da ke Gaza kisan ƙare-dangi ta hanyar amfani da makaman Amurka. Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alƙawarin sanya hannu cikin sauri kan ƙudurin na dala biliyan 61 - wanda ya hada da tallafi ga Ukraine da Taiwan - bayan da Majalisar ta ba da amincewarta ta karshe, yana mai cewa za a fara isar da tallafin da ake buƙata a wannan makon. Amurka ta bayyana goyon bayanta ga Isra'ila tun farkon yaƙin a watan Oktoban bara. Amurka ba ta taɓa ja da baya ba wajen bai wa Isra'ila makamai, ba tare da la'akari da asarar rayukan fararen hula da ake yi a Gaza ba. Amurka tana bai wa Isra'ila dala biliyan 3.8 a matsayin tallafin soji na shekara-shekara kuma galibi tana bai wa ƙawayenta garkuwa a Majalisar Dinkin Duniya. Majalisar Dattawan Amurka ta ba da tallafin dala biliyan 26.6 ga Isra'ila / Hoto: AP 2145 GMT — Isra'ila na shirin mamaye Rafah nan ba da jimawa ba - Rahoto Bayan yi watsi da roƙon da ƙasashen duniya suka yi wa Isra'ila da zargin kisan ƙare-dangi da ake mata, sojojin Isra'ila na shirin mamaye birnin Rafah da ke kudancin Gaza "nan ba da jimawa ba," a cewar kafafen yada labaran Isra'ila. A cewar kafar watsa labaran Isra'ila ta KAN, wacce ta ambato wasu majiyoyin soji da ba ta bayyana sunansu ba, rundunar sojin na shirin kai hare-hare ta ƙasa a Rafah, ciki har da "kwashe wasu mazauna yankin masu yawa." "Bisa shirin da sojojin suka yi, za a bukaci Falasdinawa sama da miliyan daya da ke Rafah da su ƙaurace wa yankin zuwa matsugunan da aka kafa kwanan nan a yankunan kudanci da tsakiyar Zirin Gaza," a cewar kafar watsa labaran.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama a sansanin Nuseirat da Rafah
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasɗinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0700 GMT — Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama a s...

Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 201. An kashe aƙalla Falasɗinawa 34,183 - galibinsu jarirai da yara da mata. An raunata wasu sama da 77,143. MDD ta ce an aikata "laifin yaƙi" bayan gano gawa sama da 300 a kaburburan bai-ɗay 0700 GMT — Isra'ila ta kai munanan hare-hare ta sama a s...
