Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai mummunan hari wata makaranta a Gaza wanda ya kashe mutum 11

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu yake kwana na 357, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,534. Bugu da ƙari, sama da mutum 620 aka kashe tun ranar 23 ga watan Satumba a wani babban harin bam da Isra'ila ta kai a Lebanon. Juma'a, 27 ga Satumban 2024 0328 GMT — Wani hari da I...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai mummunan hari wata makaranta a Gaza wanda ya kashe mutum 11
Кратко

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu yake kwana na 357, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,534. Bugu da ƙari, sama da mutum 620 aka kashe tun ranar 23 ga watan Satumba a wani babban harin bam da Isra'ila ta kai a Lebanon. Juma'a, 27 ga Satumban 2024 0328 GMT — Wani hari da I...

Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza, wanda yanzu yake kwana na 357, ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 41,534. Bugu da ƙari, sama da mutum 620 aka kashe tun ranar 23 ga watan Satumba a wani babban harin bam da Isra'ila ta kai a Lebanon. Juma'a, 27 ga Satumban 2024 0328 GMT — Wani hari da Isra’ila ta kai kan wata makaranta da ta zama mafakar dubban Falasdinawan da suka rasa matsugunansu a arewacin Gaza ya kashe akalla mutane 11 tare da raunata 22, ciki har da mata da yara, in ji Ma’aikatar Lafiya ta yankin. Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai hari a makarantar da ke sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia. Hotunan makarantar Al Falouja sun nuna yadda jami'an ceto suke ta gudu ɗauke da wadanda suka jikkata daga harabar makarantar suna kutsawa cikin tarkace da cunkoson jama'a don ceton su. Wani bidiyo ya nuna wasu mazaje suna naɗe wata gawa da ta yi rugu-rugu, suna kuma sanya sassan jikin mutane a cikin na'urar sanyaya abu. Karin bayani ???? 2050 GMT — Isra’ila ta kashe mutane 92 a sabon harin da ta kai a Lebanon Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa, Isra'ila ta kashe mutum 92 a hare-haren da ta kai a wasu yankuna na kasar Lebanon cikin sa'o'i 24 da suka gabata. A jerin bayanan da ta fitar, ma'aikatar ta ce hare-haren Isra'ila sun kashe mutum 40 a garuruwa da kauyukan da ke kudu, 48 a yankuna biyu na gabashi da hudu a gabashin tsakiyar tsaunin Lebanon. Gabaɗaya, ya ce mutum 153 sun sami raunuka. A halin da ake ciki, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kai wa a fadin kasar ya kai 1,540 tun daga watan Oktoban bara. 0152 GMT — Kuwait ta yi kashedi kan 'mummunan tashin hankali' a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Lebanon Kuwait ta ƙara nuna damuwa game da "mummunan ci gaba" da hare-haren Isra'ila ke kaiwa Labanon, tare da jaddada bukatar yin "hukunce-hukuncen siyasa na gaske na yin garambawul ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin kawar da rashin zaman lafiya a duniya." Yarima Mai Jiran Gado na Kuwait Sheikh Mishal Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York. Yarima mai jiran gado Al-Sabah ya yi Allah wadai da hare-haren da Isra'ila ta kai ta sama da kuma hare-haren soji kan kasar Labanon, lamarin da ya janyo asarar rayukan fararen hula da dama, yana mai bayyana ci gaba da ta'azzara da lamarin ke yi a matsayin keta dokokin ƙasa da ƙasa. Ya kuma soki Isra'ila da keta hurumin ƙasar Labanon da yunƙurin janyo Lebanon cikin rikicin yankin.