Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 380, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,519 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,448 a Lebanon tun Oktoban bara. Lahadi, 20 ga Oktoba, 2024 0741 GMT — Isra'ila ta kai harin bama-bamai kan asibitin Kamal Adwan a arewacin Gaza Asibitin Kamal Adwan Hospital da ke Beit Lahia ya sha ruwan bama-bamai daga hare-haren dakarun Isra'ila, wanda ke ci gaba da luguden bam a arewacin Gaza, cewar wani jami'i a yankin. Hossam Abu Safiya, daraktan asibitin ya tabbatar cikin wata sanarwa, cewa harin Isra'ila ya lalata tankunan ruwa na asibitin, da babban layin lantarki, wanda ya janyo tsayar da ayyukan kula da lafiya da dama a asibitin. Ya ƙara da cewa, yankin da ke kewaye da asibitin ya sha matsanancin luguden ruwan bama-bamai da ɓarin wuta tsawon awanni, wanda ya sanya majinyata da jami'an lafiya cikin babban haɗari. 0752 GMT — Sansanin Dakarun zaman lafiya na MDD a kudancin Lebanon ya kunna jiniyar shiga haɗari mataki na 3 An kunna jiniyar da ke nuna shiga haɗari mataki na 3, wanda ke nufin matsanancin haɗari a cikin sansanin sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) a garin Maarakeh, gundumar Tyre a kudancin Lebanon. A cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon, an yi gargaɗin ne yayin da barazana take da girma a yankin, yayin da ake ci gaba da artabu da faɗan kan iyaka tsakanin sojojin Isra'ila da ƙungiyoyin yankin. Jami'an UNIFIL da mazauna yankin sun shiga cikin barazana babba yayin da yanayin tsaro a kudancin Lebanon yake ci gaba da taɓarɓarewa. 0727 GMT — Sojojin Isra'ila sun yi iƙirarin kai hari kan hedikwatar leƙen asiri ta Hezbollah a Beirut Isra'ila ta yi iƙirarin cewa sojojinta na sama sun kai farmaki kan hedikwatar leƙen asiri ta Hezbollah, da kuma garejin aiki na ƙarƙashin ƙasa inda suke ƙera makamai a Beirut.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai harin bam kan asibitin Kamal Adwan a arewacin Gaza
Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 380, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,519 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,448 a Lebanon tun Oktoban bara. Lahadi, 20 ga Oktoba, 2024 0741 GMT — Isra'ila ta...

Yaƙin Isra'ila a Gaza yana kwana na 380, ya halaka aƙalla Falasɗinawa 42,519 da raunata kusan 100,000, inda ake tunanin mutum sama da 10,000 suna binne ƙarƙashin baraguzan gine-gine. Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 2,448 a Lebanon tun Oktoban bara. Lahadi, 20 ga Oktoba, 2024 0741 GMT — Isra'ila ta...
