Главная / Архив новостей
Архив новостей

В этом разделе представлены архивные новости с исходными датами публикации. Статья отображается на языке оригинала.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari kan taron fararen-hula a kudancin Gaza

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 322, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,265 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 93,144, kana an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Juma'a, 23 ga watan Agusta, 2024 0507 GMT –– Isra'ila ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Обновлено 13.08.2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari kan taron fararen-hula a kudancin Gaza
Кратко

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 322, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,265 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 93,144, kana an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Juma'a, 23 ga watan Agusta, 2024 0507 GMT –– Isra'ila ta...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda ya shiga kwana na 322, ya kashe Falasɗinawa aƙalla 40,265 — galibinsu mata da yara — sannan ya jikkata mutum fiye da 93,144, kana an yi amanna cewa ɓaraguzan gine-gine sun danne fiye da mutum 10,000. Juma'a, 23 ga watan Agusta, 2024 0507 GMT –– Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla huɗu, ciki har da wani yaro a hare-hare biyu ta sama da jiragen yaƙinta suka kai kan tarukan fararen-hula a kudancin Gaza da tsakar dare. Kazalika gomman mutane sun jikkata. Likitoci a Asibitin Nasser sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Falasɗinu (WAFA) cewa an kai musu gawawwakin mutum uku, ciki har da wani yaro, bayan harin da Isra'ila ta kai a garin Abasan. Bugu da ƙari, jiragen yaƙin Isra'ila sun kai hari a yankin Zaytoun a Birnin Gaza inda suka kashe mutum ɗaya tare da jikkata da dama. 0341 GMT — Harris ta yi alƙawarin 'aiwatar' da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza Kamala Harris ta yi alƙawarin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sannan ta ce idan ta zama shugabar Amurka ba za ta "ɗasa" da masu mulkin kama-karya kamar yadda Donald Trump na jam'iyyar Republican ya yi ba. "Yanzu lokaci ya yi da za a kammala yarjejeniyar sako mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma tsagaita wuta," kamar yadda mataimakiyar shugaban ta Amurka ta shaida wa magoya bayanta a taron Democratic National Convention a yayin da ta amince da tsayar da ita takarar shugaban ƙasa.