Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani jami'i na ƙungiyar ta Hamas ya bayyana. Sai dai duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta tayar da bam a unguwar Sheikh Radwan da ke cikin birnin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa 10. Wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari kan wani gida mallakar iyalan as-Sardi da ke unguwar inda farar hula 10 suka rasu, wasu kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra'ila WAFA ya tabbatar. 0030 GMT — An gudanar da zanga-zanga 105 a biranen Morocco 48 domin nuna goyon baya ga Gaza An gudanar da zanga-zanga 105 a ranar Juma'a a biranen Moroko 48 don yin tir da hare-haren Isra'ila da nuna goyon baya ga Gaza. Dubban jama'a ne suka taru a wuraren da jama'a ke yin zanga-zangar domin amsa kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, ciki har da hukumar kare muradun al'ummar kasar Morocco. Masu zanga-zangar sun nuna bacin rai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu
Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari Gaza a daidai lokacin da wakilan Hamas suka tafi Masar tattaunawar tsagaita wuta
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahi...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara. 0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahi...
