Mwanzo / Kumbukumbu za habari
Kumbukumbu za habari

Sehemu hii inaonyesha habari za kumbukumbu pamoja na tarehe zake za awali za kuchapishwa. Habari imeonyeshwa katika lugha yake ya asili.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari a wani gida a Gaza, ta kashe Falasɗinawa da dama — rahotanni

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 394 — ya kashe mutane aƙalla 43,314 da jikkata fiye da mutum 102,019, sannan fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Israila ta kashe mutum 2,968 tun daga Oktoban bara. Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2024 0058 GMT — Isra'il...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Imesasishwa 13/8/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari a wani gida a Gaza, ta kashe Falasɗinawa da dama — rahotanni
Kwa muhtasari

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 394 — ya kashe mutane aƙalla 43,314 da jikkata fiye da mutum 102,019, sannan fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Israila ta kashe mutum 2,968 tun daga Oktoban bara. Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2024 0058 GMT — Isra'il...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 394 — ya kashe mutane aƙalla 43,314 da jikkata fiye da mutum 102,019, sannan fiye da 10,000 na danne a ƙarƙashin ɓaraguzai. A Lebanon, Israila ta kashe mutum 2,968 tun daga Oktoban bara. Lahadi, 3 ga watan Nuwamba, 2024 0058 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa da dama tare da jikkata gommai a harin bam da dakarunta suka kai da sanyin safiyar ranar Lahadi a wani gida da ke yankin Tal al-Hawa na kudu maso yammacin Birnin Gaza. Kamfanin dillancin labaran Falasɗinawa, Wafa , ya ambato majiyoyi da dama a yankin suna cewa Isra'ila ta kashe mutane da yawa da jikkata gomma bayan ta rurga bama-bamai a gidan Abu Al-Auf da ke Tal al-Hawa, inda aka rika yi wa ma'aikatan agaji kiran gaggawa domin su kai ɗauki a gidan. Tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara ne Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza, inda ta yi wa ɗaukacin yankin ƙawanya. Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 43,314, sannan an yi amanna dubbai na binne a ƙarƙashin ɓaraguzai.