Home / News archive
News archive

This section shows archived news with its original publication dates. The article is displayed in its original language.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari a kudancin Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 10

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 454 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,553 da jikkata mutum fiye da 108,379. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025 0028 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinaw...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Updated 13/08/2026, 05:26:13
Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari a kudancin Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 10
At a glance

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 454 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,553 da jikkata mutum fiye da 108,379. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025 0028 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinaw...

Yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 454 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 45,553 da jikkata mutum fiye da 108,379. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,048 tun daga Oktoban 2023. Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025 0028 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa aƙalla goma a wani hari da ta kai a tantin da wasu mutane da ta kora daga gidajensu suke samun mafaka a kudancin yankin Gaza da aka mamaye, a cewar ma'aikatan kiwon lafiya. Mutanen 10, ciki har da mata da yara, sun mutu ne a tantin Al-Mawasi, wanda aka ayyana a matsayin wurin bayar da agaji ga mutanen da suke buƙatar agajin gaggawa a Khan Younis da ke yammacin Gaza, in ji jami'an asibiti. Sun ƙara da cewa an jikkata mutum goma sha biyar. Ƙarin labarai ???? 0009 GMT — Sojojin Isra'ila sun jikkata Falasɗinawa 3 a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan Sojojin Isra'ila sun buɗe wuta yayin wani samame da suka kai Tsohon Birnin Nablus da ke arewacin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan, inda suka jikkata mutum uku. Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasɗinu ta ce an kai mutanen Asibitin Gwamnati na Rafidia da ke Nablus. Ma'aikatar ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka jikkata ya samu munanan raunuka na harbin bindiga, yayin da biyu kuma suka samu ƙananan raunuka a ƙafa da cinya.