Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 1011 GMT —Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Palestinian Red Crescent Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a ginin kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent Society (PRCS) inda suka kashe mutum guda tare da jikkata mutum shida. Kungiyar ta wallafa bidiyo da ya nuna cewa harin ya sauka a gininta da ke birnin Khan Younis. Kungiyar ta PRCS, wadda ke bayar da agajin magunguna da na jinkai, ta fuskanci hare-hare a yakin da Isra'ila ta kaddamar a Gaza. Kazalika Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14, ciki har da kananan yara tara, a jerin hare-haren da ta kai a yammacin birnin Khan Younis na Gaza, a cewar ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin. 0150 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza Sojojin Isra'ila sun yi harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da luguden bama-ba masu nauyin sama da tan 65,000 tonnes a yakin da take yi a Gaza, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza. "Jiragen yakin sojoji mamaya sun harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da manyan bama-bamai, wasu daga cikinsu na da nauyin tan dubu biyu, a hare-haren kare-dangi na yakin da suka yi a Zirin Gaza, kuma da gangan suke kai hari kan gidaje," in ji ofishin. "Nauyin bama-baman da sojojin suka harba a Zirin Gaza ya zarta tan 65,000, wanda ya fi nauyin bama-baman nukiliya guda uku da aka jefa a birnin Hiroshima na kasar Japan." Ofishin ya ce kusan kashi "biyu cikin uku na bama-bamai da makamai masu linzamin...ana harba su ne a ko'ina ba tare da kiyaye kowanne wuri ba." Iirin barnar da jiragen yakin Isra'ila suka yi a Gaza sakamakon luguden wutar da suke yi ta sama./Hoto:OTHER 0100 GMT — Wani jami'in gwamnatin Biden ya ajiye aiki saboda goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila Wani jami'i a Ma'aikatar Ilimi ta Amurka ya ajiye mukaminsa saboda yadda Shugaba Joe Biden yake goyon bayan Isra'ila a luguden wutar da take yi a Gaza da ta mamaye, wata alama da ke nuna rabuwar kawuna a gwamnatin kasar. Tariq Habash, mataimakin na musamman a fannin Tsare-Tsare na Ma'aikatar Ilimi, a wata wasika da ya aike wa Sakataren Ilimi Miguel Cardona, ya ce: "Ba zan iya ci gaba da yin gum da bakina ba a yayin da gwamnati ta rufe idanunta game da hare-haren da ake kai wa Falasdinawa da ba su da laifi, abin da masu kare hakkin dan'adam suka bayyana a matsayin kisan kare-dangi da gwamnatin Isra'ila ke yi." "Ba zan kasance cikin masu aikata laifi a yayin da wannan gwamnatin ta gaza yin amfani da matsayin wajen hana babbar kawarta Isra'ila ci gaba da cin zarafi a Gaza tare da katse hanyoyin samun abinci da ruwa da lantarki da fetur da magunguna, lamarin da ya haddasa cutuka da yunwa," in ji Habash.
أرشيف الأخبار
يعرض هذا القسم الأخبار المؤرشفة مع تواريخ نشرها الأصلية. يُعرض المقال بلغته الأصلية.
KAI-TSAYE: Isra'ila ta kai hari a ginin kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 1011 GMT —Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Pa...

لمحة سريعة
Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 1011 GMT —Isra'ila ta kai hari a ofishin kungiyar Pa...
