Ana Sayfa / Haber arşivi
Haber arşivi

Bu bölüm arşiv haberlerini özgün tarihleriyle gösterir. Haber metni özgün dilinde gösterilmektedir.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 0150 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin ta...

NewstimeTR Haber Merkezi · · Güncellendi 13.08.2026 05:26:13
KAI-TSAYE: Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza
Bu haberde ne var?

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 0150 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin ta...

Hare-haren da Isra'ila ta kwashe kwana 89 tana kai wa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 22,313 da jikkata mutum 57,296 a yayin da Tel Aviv ke ci gaba da luguden wuta a birane da garuruwa da sansanonin 'yan gudun hijira na yankin. 0150 GMT —Isra'ila ta jefa bama-bamai masu nauyin tan 65,000 a 'yakin kare-dangi' na Gaza Sojojin Isra'ila sun yi harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da luguden bama-ba masu nauyin sama da tan 65,000 tonnes a yakin da take yi a Gaza, a cewar Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza. "Jiragen yakin sojoji mamaya sun harba makamai masu linzami fiye da 45,000 da manyan bama-bamai, wasu daga cikinsu na da nauyin tan dubu biyu, a hare-haren kare-dangi na yakin da suka yi a Zirin Gaza, kuma da gangan suke kai hari kan gidaje," in ji ofishin. "Nauyin bama-baman da sojojin suka harba a Zirin Gaza ya zarta tan 65,000, wanda ya fi nauyin bama-baman nukiliya guda uku da aka jefa a birnin Hiroshima na kasar Japan." Ofishin ya ce kusan kashi "biyu cikin uku na bama-bamai da makamai masu linzamin...ana harba su ne a ko'ina ba tare da kiyaye kowanne wuri ba."