Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yanzu ya shiga kwana na 312, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,897 — yawancinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 92,152, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 13 ga watana Agusta, 2024 2207 GMT — Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana girman mamayar da sojojin Isra'ila suke yi wa yankin Gaza, tana mai cewa an kori kusan kashi 84 daga yankin. Da yake bayani kan alƙaluman da Ofishin Babban Mai Kula da Harkokin Jinƙai na Majalisar (OCHA) ya tattara, mataimakin kakakin ofishin Farhan Haq ya shaida wa manema labarai cewa "luguden wuta da kuma kutsen da Isra'ila take yi a Gaza na ci gaba da kashewa da jikkatawa tare da korar Falasɗinawa daga matsugunansu – da kuma rusa gidajensu da sauran gine-gine da suka dogara a kansu." Ya ce, "Sau biyu sojoji suna bayar da umarni ga mutane su fita daga Khan Younis a ƙarshen mako, zuwa yankunan da a baya galibi aka umarci mutane su fice daga cikinsu." Wannan lamari ya shafi yankuna 23 da wurare 14 da ke samar da ruwa da tsaftar jama'a da kuma makarantu huɗu. "Jimilla, sojojin Isra'ila sun kori mutane daga wurin da ya kai girman murabba'in kilomita 305, wato kusan kashi 84 na yankin Zirin Gaza," in ji shi. 2335 GMT — Wata 'yar siyasa a Finland ta soki gwamnati kan ƙin ɗaukar mataki a yaƙin Gaza Nasima Razmyar, mataimakiyar shugaban jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) ta Finland kuma 'yar majalisar dokoki, ta caccaki gwamnatin ƙasar kan gaza sukar Isra'ila bisa kisan kiyashin da take yi a Gaza, inda ta zargi mahukunta a Helsinki da zama 'yan amshin-shata, kamar yadda kafofin watsa lamarai suka ruwaito. Razmyar ta bayyana matuƙar ɓacin ranta kan kisan ƙare-dangin da Isra'ila take yi wa Falasɗinawa da kuma rashin kataɓus na ƙasashen duniya. "Rashin imanin da ake yi a yaƙin Gaza abu ne da ba zai misaltu ba. Mun zama kamar kurame, Al'umma na ɗanɗana kuɗarsu, suna fama da bala'in yunwa sannan gidajensu sun zama toka— wannan lamari ne da ke da wahalar fahimta domin kuwa ko da yaushe a cikin yaƙi suke," kamar yadda jaridar Helsinki Times ta ambati ta tana cewa. 'Yar siyasar ta ce duk da kiran da Kotun Ƙasa da Ƙasa ta (ICJ) ta yi kan a tsagaita wuta da kuma bayyana mamayar da ake yi wa yankunan Falasɗinawa a matsayin haramtacciya, Isra'ila tana ci gaba da kashe su.
Cette rubrique présente les archives avec leurs dates de publication originales. L’article est affiché dans sa langue d’origine.
Kai-tsaye: Isra'ila ta bai wa 84% na Falasɗinawan Gaza umarnin barin gidajensu — MDD
Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yanzu ya shiga kwana na 312, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,897 — yawancinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 92,152, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 13 ga watana Agusta, 2024 2207 GMT — Majal...

Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza, wanda yanzu ya shiga kwana na 312, ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa aƙalla 39,897 — yawancinsu mata da yara — tare da jikkata mutum sama da 92,152, kana an ƙiyasta cewa fiye da mutum 10,000 na danne a ɓaraguzai. Talata, 13 ga watana Agusta, 2024 2207 GMT — Majal...
